Sabon gwamnan Jahar Bauchi da aka rantsar, Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar ya ce gwamnatin Malam Isa Yuguda da ta shude, ba ta bar komai a baitul malin jahar ba.
Sabon gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin jawabinsa na farko bayan da aka rantsar da shi a jiya Juma'a.
“Mun karbi baitul malin da babu aninin toka a cikinsa, saboda haka muna rokon jama’ar jahar Bauchi su yi mana hakuri.” Inji Barrister Abubakar.
Ya kara da cewa ba za su “gudu ba” duk da cewa sun san aikin yana da wuya saboda akwai bukatar a fidda jahar daga cikin kangin da ta shiga.
A Jahar Gombe da ke makwabtaka da jahar ta Bauchi, gwamna Ibrahim Hassan Dan Kwambo, da aka zaba a wa’adi na biyu, ya kara baiwa jama’ar jahar hakuri ne da neman goyon baya.
“In kira ga jama’ar jahar Gombe da a dada bamu goyon baya a dada yin hakuri domin a kara samun ci gaba kamar yadda aka samu a shekarun da suka gabata.” Inji Dan kwambo.
Ya kuma kara da cewa ya san a “matsayinsa na dan adam” ya tafka kura kurai saboda haka ya nemi jama’r jahar da su yafe masa.
“A matsayi yi na dan adam, na yi kuskure da dama, nima ina kira ga al’umar jahar Gombe da ina so ku yafe mini.” Dan Kwambo ya ce.
Title :
Yuguda Bai Bar Ko Sisi Ba- Gwamna Abubakar
Description : Sabon gwamnan Jahar Bauchi da aka rantsar, Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar ya ce gwamnatin Malam Isa Yuguda da ta shude, ba ta bar kom...
Rating :
5