Tiyatace katuwa kimanin mutane dubu hudu da dari biyar ne zaune,sun sa ido suna kallon saman matsayar malamai.Mussadik ne tsaye duk yayi gumi,daga gefensa malaman wannan jami'ar ne duk suntaru suna sauraren shi.Shidai mussadik Yusuf,dalibine dake karantar ilimin na ura mai kwakwalwa watau computer.Ana zargin mussadik da cin zarafin mata,da musguna musu,halinsane idan ana lacture kaganshi can saman kujeru shi kadai a gefe.Wasu na tunanin tsabar iya lissafi da yawanyinsane yasa kwakwalwar mussadik ta tabu,ammafa duk lalubene a duhu,domin idan kayi mu'amala dashi sai kaga abin da ake fada akansa karyane,dominko mutumne na tsatse gashi da kula da addini,matsalarsa dayace,baya magana da mata,kuma idan sukashiga gonarsa,baya yi musu ta dadi.Wata rana Aseeya sulaiman ta samu mussadik a zaune gindin wata bishiya yana zaune yana karatu,tayi masa sallama,yanaji macece yayi shiru yaki ya amsa,ta matso tace"haba Mussadik kamar ba musulmiba nayi sallama kaki amsawa?yayi shiru kamar tana magana da dutse,tayi surutanta tagaji yayi banza da ita.Tana tafiya wasu hawayen takaici suka zubomai,yace"wawiya kinci sa'a yau jumu'a ranar farin cikice da naci miki mutunci,amma Allah ya kara kawoki,sai naci mutuncinki.Aseeya na zuwa common room ta tarar da kawayenta suna zaune,tana zuwa Jameela ta kalleta tace"oh ke mutumin daya tsani mata kekuma shi kikeso?mariya tace"Ni tsakanina da wannan ai kawai yawuce na wuce,ba kyagani ko a aji muke baya zama kusa da kowa.Aisha tace"Aseeya rabu dasu ni nasan abin dayasa take sonshi,na farko Aseeya Ustaziyace,shiyasa take bukatar namiji mara kula mata,gata da kishi kunga hakan zaisa ta samu na tsuwar zuciya,suka sheke da dariya,sukace to ayi mugani idan tusa zata hura wuta.Wataki nawa kina yi mai magana amma ko sauraronki bai taba yiba?Aseeya tace ai ba'a samun abu mai daraja cikin sauki sai ansha wuya.Wata rana Aseeya ta zo makaranta bata tsaya ko inaba sai inda Mussadik yake zama dan shan iska,tana zuwa tai mai sallama,yanajin kamshin turaren data sawo yaji kwakwalwarsa ta buga kansa ya kama ciwo.Aseeya tace"nasan ina damunka bisa yadda nake bibiyarka amma dan Allah kayi hakuri,ba wani abu yasa naketa damunkaba illa kasani Allah s.w.a ya jarabceni da mutukar so da kaunarka,wlh bantaba sanin haka so yakeba sai dana fada cikinnaka,kasani ya kai mussadik kullum nai bacci sai nayi mafarkinka,kuma wallahi komai na kalla sai inga hotonka,kataimaki rayuwata,ka damki sona da kauna da hannun dama,kasani zan iya shiga wani hali idan harka kini.Tana rufe baki taji wani mari afuskarta"ya dubeta yace"angayamiki dadin bakinku zai kima tasiri akainane?to ki saurareni,idan kika kuskura kika kara furtamin wata kalma da tai kama data wani banzan abu wai shi so wlh sai nayi miki abin dayafi haka.Zafin marinsa bai damu Aseeyaba abin da yafi yi mata ciwo shine,tadauki lokaci tana sonsa amma sai yau ta iya furtamai domin idan tacigaba da boye sonsa zata iya kamuwa da ciwon zuciya,to ashe hakan ma ba mafita bace.Mussadik na wucewa yabarta ta fadi sumammiya mutane sukazo,suka kewayeta,shiko ko waige baiyiba,kawayenta nazuwa suka daukeya sai gida,suna zuwa Alhji sulaiman ya kira likitansa dan yazo ya duba Aseeya,kafin yazo Aseeya ta mutu.Kashe gari Mussadik na shigowa makaranta,abokinsa Hamza yasameshi yasanar dashi abin dake faruwa,nan da nan idanuwansa suka ciko da hawaye,ya kama wani sambatu yana fadin"banyi mata haka dan musguna mataba sai dan tasamu yakinin cewa ni babu wata kalma so a kundin rayuwata.Suna tsaye security sukazo suka kamashi,suka kaishi gurd room suka kulle.Bayan makaeanta tayi bincike sai ta gano ashe dama Aseeya tana da ciwon zuciya,Mussadik ya taka sawun barawone kawai.Babanta yace duk dacewa shi ya karasata amma munsani dukkan dan adam zai dan dana mutuwa,sabo da haka mun yafe mai.Makaranta da iyayen Aseeya duk sunyafe wa mussadik amma da sharadin sai mussadik ya bayyana sirrin dayasa ya tsani mata,ya ki jininsu kuma yake musguna musu,gami da rashin son mu'amala dasu.Makaranta duk ta dauka cewa"yau ne ranar da mussadik zai gurfana gaban kowa da kowa dan bayya dalilinsa na tsana da tsar gar mata.wannan yasa kowa daga makarantar ya hallara,a yanzu kimanin mutum dubu takwasne ke zaune wasu a tsaye suke ta sauraro da kuma kallon Mussadik Yussuf,shiko gumi kawai yake.Mussadik ya rike microphone,ya daga kai ya dubi jama'ar dake gabansa sai ya fashe da kuka,azuciyarsa yace"yanzu duk mutanennan sai sunji sirrina?yace to ya zanyi.
Mussadik yayi gyaran murya yace"mai girma shugaban wannan Jami'a masu girma shugabannin wannan jami'a,masu girma profs na wannan jami'a,masu girma doctors na wannanjami'a,yan uwana dalibai na wannan jamia inai muku gaisuwa.
Na tsaya agabankune dannasar daku dalilin dayasa na tsani mata ko nake musgunawa mata.
Da farko dai Sunana mussadik Yusuf;an haifeni agarin Kipa.Daliln dayasa na tsanimata ko nake musguna musu shine,yadan tsaya kan ya fashe da kuka,sannan yaci gaba dacewa.