Ranar Juma’ar da ta gabata da misalin kafe 8:30 zuwa tara na dare wasu ‘Yan Sanda suka harbe wani yaro Yasir Rabiu a unguwrsu ta Gyadi Gyadi. Wannan al’amari ya faru bayan sallar Magariba lokacin da wannan yaro dan shekara ashirin da haihuwa wanda yake makarantar Karamar Sakandiren Gwamnati ta Gyadi Gyadi.
Yasar Rabiu ya Isa Kofar wata makarantar Islamiyya mai Suna Abdulkadir Islamiyya sai kawai suka hangi ‘yan sanda sun shigo wannan layi a sukwane, sannan kuma suka fara harbi. Marigayin wanda ke kan hanyarsa ta sayen katin waya sai kawai jin harsashi ya yi a kirjinsa da kuma guiwar kafarsa.
Hakan ta sa ya fadi kasa yayin da sauran jama’a kowa ya fara gudun tsira da rai. Mahaifin marigayin mai Suna Malam Rabiu wanda wakilinmu ya same shi cikin dimuwa tare da tsananin damuwa ya shaidawa wakilinmu cewar suna gida suka ji karar harbi, jimawa kadan sai ya ji an yi sallama a na cewa nan ne gidan su Yasar sai kawai a ka shigo da shi cikin jini yana ta kwarara.“Ganin haka muka yi salati, a dai-daita sahun da ta kawo shi ita muka wuce da ita zuwa asibitin Malam Aminu Kano, a lokacin da a ke kokarin yi masa aiki domin fitar da harsashen hudu da suka same shi ya ce gagarinku.”
Malam Rabi’u ya kuma bayyanawa LAEDERSHIP Hausa cewar Yasar yaro ne mai hankali ga ladabi da biyayya, saboda haka ya yi addu’ar fatan Allah ji kansa da gafara.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Kano Magaji Musa Majiya wanda ya bayyana cewar “Ranar juma’a da ta gabata DPO da yake kula da filin Hocky tare da jami’an tsaro har da ‘yan banga sun kai samame wani waje wanda yake matattarar ‘yan daba ce, ya ce makwabtan wurin sun yi takai korafi ga hukumar ‘yan sanda saboda yadda a ke kwace tare da fyade.’
Ya ce “Zuwansu wannan wuri sai matasan suka fara ihu suna jifar ‘yan Sanda har suna fasa kwalabe. Haka tasa wani jami’in ‘yan sanda mai mukamin Kofur mai suna Abdul Yahaya ya yi harbi wanda ya samu wani yaro mai suna Yasar Rabiu. Bayan kai shi asibiti da safiyar yau aka sanar a damu cewar ya rasu.” Ya bayyana.
Title :
‘Yan Sanda Sun Harbe Yaro Har Lahira A Kano
Description : Ranar Juma’ar da ta gabata da misalin kafe 8:30 zuwa tara na dare wasu ‘Yan Sanda suka harbe wani yaro Yasir Rabiu a unguwrsu ta Gyadi Gyadi...
Rating :
5