Wasu 'yan gudun hijira da kuma 'yan ci-rani wadanda suka isa Indonesia sun ce fadan da ya barke a jirgin ruwan da suke ciki sakamakon takaddama kan abinci ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 100.
Da suke magana a wani sansani a Aceh sun shaida wa BBC cewa wasu mutanen an soke su da wuka, wasu aka rataye su, wasu kuma aka jefa su cikin teku.
Yana da wuya dai a iya tantance gaskiyar labarin, sai dai kuma ya zo daidai da rahotannin da wasu kafofin yada labarai suka bayar.
Ana tsammanin dubban 'yan gudun hijirar daga Bangladesh da kuma Myanmar suna rito akan teku tsakanin Thailand da Indonesia da kuma Malaysia bayan da wadanda suka yi safarar su suka yi watsi da su.
Title :
Yan ci-rani sun mutu a fada kan abinci'
Description : Wasu 'yan gudun hijira da kuma 'yan ci-rani wadanda suka isa Indonesia sun ce fadan da ya barke a jirgin ruwan da suke ciki sakamako...
Rating :
5