Rahotanni daga jihar Filato a Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun sace shanun Fulani makiyaya kimanin 900, suka kuma bindige wani makiyayi har lahira a karamar hukumar Wase.
Barayin sun dirar wa makiyayan ne da bindigogi a ranar Lahadi, suka yi awon gaba da dabbobin.
Sakataren kudi na kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah a jihar Filaton, Malam Salihu Jauro, ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa an sace shanun, kuma an kashe makiyayi daya da jikkata wani guda.
Shi ma kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Abuh Emmanuel, ya tabbatar da satar shanun, amma ya ce bai samu bayanin adadin shanun da aka satan ba da kuma yadda lamarin ya faru.
Satar shanun a yankin Wase dai ya zo ne kwanaki biyu kacal bayan sace shanun Fulani kimanin 600 a karamar hukumar Ibi ta jihar Taraba mai makwabtaka, inda a wancan lamarin ma Fulanin suka yi zargin cewa an kora dabbobin ne zuwa kudancin jihar Filato.
Matsalar satar shanu dai na daya daga cikin abubuwan da ke haddasa rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini a jihohin na Filato da Taraba.
Source bbchausa
Title :
Yan bindiga sun sace shanu 900 a Filato
Description : Rahotanni daga jihar Filato a Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun sace shanun Fulani makiyaya kimanin 900, suka kuma bindige wani maki...
Rating :
5