Shi dai Aljanin soyayya yana da mutukar naci da kuma bala'in taurin kai. haka shima Aljanin sihiri. Don hakane tare da taimakon Allah, ZAUREN FIQHU ya hada wani man shafawa na musamman domin tunkarar matsalarsu.
Idan Aljani ya dameki kullum yana zuwa yana saduwa dake acikin barci, ko afarke, ko kuma anyi miki sihiri an hadaki da wani Shaitanin Aljani, Ga yadda zakiyi amfani da maganin domin neman lafiyarki in sha Allah:
1. Ki samu tufafi na musamman wanda kika wareshi domin kwanciyar barci. Sai ki dauko robar da MUHRIQUL JINNI yake ciki, ki shafe dukkan tufafin dashi. Sannan ki mayar ki ajiye sai lokacin barci yayi ki dauko ki sanya.
2. Ki tabbatar kinyi alwala kin tsane jikinki kafin barci. Ki dauko maganin Ki shafa dukkan jikinki. Musamman ajikin dukkan Qofofi talatin da suke jikinki. Wato:
- Yatsun hannaye da Qafafu, har karkashin farce. (kofofi ashirin ne chif).
- Idanunki biyu.
- Kunnuwanki biyu.
- kofofin hancinki.
- Gefen bakinki.
- Ramin cibiyarki.
- Kofofin kan nono guda biyu.
Idan an hada gaba daya sun zama kofofi talatin kenan. Kofar dubura da farji, kar ki sanya Muhrikul jinni. tunda anyi karatu acikinsa. sai dai ki nemi JAN ALMISKI ki shafa a kofar dubura, da kuma farji.
2. Ki tabbatar kinyi BISMILLAH yayin da zaki shafa akowacce Kofa. Kuma ki shafa acikin kitsonki ma sosai.
3. ki dauko wannan rigar varcin ki sanya kiyi addu'ar barci (Ayatul kursiyyi, falaki da Naasi, da sauran azkar). Sannan ki kwanta akan gefenki na dama. Kuma kici gaba da ambaton Allah har barci ya daukeki.
4. ki kiyayi komawa barci bayan sallar asubah. yana da hatsari sosai gareki. Domin awannan lokacin ne Aljanu sukan samu nasara akan Mataye da dama.
In sha Allahu zaki samu kariya sosai daga sharrinsu. kuma Aljanin zai rika konewa har gari ya waye. Watakil ma daga sannan ya rabu dake kenan har abada. In ma sihirin ne Allah zai karyashi.
A dogara ga Allah shine fiyayyen abin dogaronmu.
DAGA ZAUREN FIQHU