Dimbin godiya gare ku masu karatu, bayan doguwar mahawarar da a ka tafka dangane da makalar da na muka wallafa a wannan shafin kimamin makwanni uku baya, mai taken ‘Kilu Ta Ja Bau: Yadda Kishi Ke Janyo Wa Matan Aure Salula,’ na yi ta samun martani, korafe-korafe da sauransu musamman daga mata. Yawanci sukan yi korafi kan abin da suka kira ‘son kai.’ Sun zarge ni da ba wa mazajensu kwarin gwiwar neman mata a waje, ko kuma auren mata na daban. A yayin da wasu kuma suka yaba da irin shawarwarin da aka bayar, gami da neman ya kamata su ma mazan, a shirya musu makala ta musamman kan cin zarafin aure, tauye hakki da rashin kulawar da suke nuna wa matansu na gida. Ko kuma suke fifita matan waje kan na su na Sunnah.
Hakikanin gaskiya, na yaba da dukkanin bangarorin, kuma bisa alkawari, ina nan ina gudanar da bincike kan makalar tare da neman karin bayani, musamman kan maza. Da yardar Allah za a karanta rahoton nan gaba kadan. Na gode da dimbin shawarwarinku da goyon baya. Allah ya bar zumunci.
A yau kuma, so nake mu nemi bakin zare kan wasu sirruka na ma’aurata. Na jima ina wani tunani… Shin mene ne sirrin zaman lafiya tsakanin miji da mata? Mene ne ke sa aure samun karko, ba ya baci bare ya lalace? Tambayoyin dai ga su nan ba adadi… kan irin sirrukan da ke tsakanin ma’aurata.
Amma a gurguje, ina son mu kalli wadansu al’amura guda biyu masu kishiyantar juna a rayuwa, su ne kamar haka: DADI da WAHALA. Shin mene ne tasirinsu a zaman aure? Ko za su iya taka wata rawa wajen kara dankon zaman, ko ruguza katangar alkawarin?
Na sha tambayar ma’aurata daban-daban: Ko DADI na iya zama silar tabbatar mace dindindin gidan miji? Na biyu – Ko WAHALA na iya korar mace daga gidan miji?
Wadannan su ne abubuwan da ke shige wa jama’a da daman gaske duhu dangane da zamantakewar aure.
A nawa binciken da nazari, na gano cewa DADI, ma’ana wadata mace da komai na rayuwar jin dadi, ba shi ne ke tabbatar da zaman lafiya ba. Haka kuma WAHALA, ma’ana gallazawa mace ba shi ke ruguza zaman na aure ba.
Tun da haka ne, shin mene ne SIRRIN MA’AURATA? Masu hikima sun ce, mata yaryadi ne, dadi ba zaunar da su, haka kuma wahala ba ta korarsu. Yaryadi a nan, wata ciyawa ce mai wuyar sha’ani, wadda nan da nan za ta iya tadiye mutum komen girmansa, ta kayar da shi kasa.
source: leadershiphausa
Title :
Ya Auri Mata Biyu Rana Daya, Lokaci Guda
Description : Dimbin godiya gare ku masu karatu, bayan doguwar mahawarar da a ka tafka dangane da makalar da na muka wallafa a wannan shafin kimamin makwa...
Rating :
5