Wikki Tourist ta Bauchi ta lallasa Enugu Rangers da ci 4-2 a gasar Premier Nigeria wasan mako na bakwai da suka yi ranar Lahadi. 'Yan wasan da suka ci wa Wikki kwallayen sun hada da Christopher Waziri da Uche Martins sai Mubarak Umar wanda ya zura kwallaye biyu a karawar Yayin da Godwin Aguda da Bobby Clement suka ci farke wa Rangers kwallaye biyu a wasan.
Rangers ta karasa karawar ne da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Etim Matthew jan kati minti 13 da aka dawo daga hutun rabin lokaci. Ita kuwa Kano Pillars ta yi rashin nasara ne a hannun Kwara da ci daya mai ban haushi, Sunshine ta casa Heartland da ci 3-0 har gida.