Babban makiyinka shine ZUCIYAR NAN TAKA wacce kullum take zugaka tana Qara janyoka cikin sabon Allah.
Ko shaitan ba ya samun nasara akanka sai ya hada kai da ita.. sai da taimakonta yake cin nasa tree a akanka. Domin ita take bashi wajen zama.
Zuciyarka ita ce take zugaka tana gaya maka cewa "KAI WANI NE". Daga nan sai ta tura Qeyarka zuwa ga GIRMAN KAI, TAQAMA, FARIYA, da sauransu.
Ita ce kullum take mantar dakai kusancin ajalinka, da kusancin Ubangijinka... Tana gaya maka cewa "KA SHEKE AYARKA KAWAI.. AI KANA SA A SAURAN LOKACI. AI KODA ZAKA TUBA BA YANZU BA TUKUNNA.. SAI KA TSUFA".
Ka manta cewar ga Mala'ikan mutuwa nan ya biyoka aguje, ga ayyukanka nan tare dakai ko yaushe tamkar inuwarka, sannan ga Qabarinka nan ya bude baki Kamar Damusa... yana jiran afkawarka inda zaka zauna daga kai sai aikinka wanda ka aikata. (ALKHAIRI KO SHARRI).
'yan uwa arage burin zaman duniya, arika kokarin gyara gidan lahira domin shine tabbataccen Mazauni. Don haka mu tuba zuwa ga Allah gaba dayanmu domin mu samu rabauta.