Mutumin da ya fi kowa arziki a Afrika, Aliko Dangote ya ce har yanzu yana da sha'awar sayen hannun jari a kungiyar Arsenal ta Ingila.
A shekara ta 2010, ya yi yunkurin sayen wani bangare na Arsenal din amma kuma sai abin bai yiwu ba.
Dangote wanda arzikinsa ya kai dala biliyan 15.7 ya kasance mai goyon bayan Arsenal na tsawon shekaru.
"Ina saran wata rana zan sayi kulob din a kan farashin da ya dace," in ji Dangote a hirarsa da Bloomberg.
Ya kara da cewar "Watakila in saya amma ba a tsawwalallen farashi ba kuma a kan farashin da ya dace."
Dangote mai shekaru 58, idan har ya samu nasarar sayen Arsenal to zai shiga cikin sawun attajirai 'yan kasashen waje da suka mallaki kungiya a Ingila kamar dan Rasha ,Roman Abramovich mai kungiyar Chelsea da kuma Sheikh Mansour bin Zayed al Nahyan na Abu Dhabi wanda ya sayi Manchester City.
Title :
Wata rana zan sayi Arsenal - Dangote
Description : Mutumin da ya fi kowa arziki a Afrika, Aliko Dangote ya ce har yanzu yana da sha'awar sayen hannun jari a kungiyar Arsenal ta Ingila. A...
Rating :
5