Ranar Juma’ar da ta gabata ne wani magidanci mai suna Malam Muhammadu Lauwali, wanda aka fi sani da “Fura ke aiki” da ke zaune a Unguwar Allugu a cikin garin Argungu da ke jihar Kebbi ya shiga kundin tarihin wadanda aka haifa ma ’ya’ya uku a lokaci guda.
Wakilinmu ya garzaya gidan, inda kuma magidancin a cikin farin ciki ya bayyana godiyar sa ga Allah da wannan baiwa da ya yi masa. Ya ce lamarin ya soma ne tun ranar Alhamis da misalin karfe goma na dare, a lokacin da matar tasa ta gaya masa ba ta jin daidai a cikin. Daga nan sai ya dauke ta zuwa gidan Hajiya Fatima Muhammed da aka fi sani da Malama Chimata, wata tsohuwar ma’aikaciyar asibiti da ta yi fice wajen taimaka wa mata, musamman masu juna biyu, da kuma wajen haihuwa.
Bayan ta dubata, sai ta ce da shi haihuwa ce, saboda haka sai su je asibiti. Bayan ya kai ta asibiti cikin daren Alhamis din, da gari ya waye ranar Juma’a da misalin karfe goma na dare sai aka shaida masa cewa matarsa ta haifi ’ya’ya uku, kuma lafiya kalau.
Ya ci gaba da cewa, an haifi yaran duka uku da suka kunshi mata biyu da namiji daya lafiya kalau, ba tare da an yi wa matar aiki ba, sannan kuma duk lafiyar su kalau, illa dai a matsayinsa na talaka ya nemi tallafi don dawainiyar ’ya’yan da mahaifiya daga hukumomi da kuma masu hannu da shuni.
Sai dai Malam Lauwali ya karyata maganar cewa ana ba mata masu juna biyu magani kyauta a jihar Kebbi, saboda shi kam hatta da allurorin da ake yi, shi ne ya saya da kudinsa, tun lokacin da ya kai matarsa asibitin har zuwa lokacin da haifu.
Mahaifiyar yaran, Malama Sadiyya Lauwali ta bayyana wa wakilin mu cewa duk da kasancewar wannan haihuwar ita ce ta biyar, amma ba ta ji bambancinsa da na farko ba, tun kama daga wajen renon cikin har zuwa lokacin haihuwar.
Malama Sadiyya ta yi kira ga mahukunta da sauran kungiyoyin mata, da kuma masu hannu da shuni su tallafa mata duk hanyar da za su iya, saboda mijinta talaka ne, kuma tana fama da rashin ruwan nono, don ta sami saukin shayar da su.
Wata majiya daga asibitin, ta shaida wa waklinmu cewa duk da yake ’ya’yan na watanni bakwai ne, amma suna cikin koshin lafiya. Sai dai mahaifiyar da jinjiran suna bukatar abubuwan da ke gina jiki.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Shugaban Karamar Hukumar Argungu, Alhaji Salihu Ahmed KC, amma bai same shi ba. Sai dai Daraktan kula da walwala da jin dadin jama’a na Karamar Hukumar, Alhaji Yusuf Musa ya bayyana cewa tuni Karamar Hukumar ta soma shirye-shirye don kai masu dauki, kamar yadda aka saba idan irin wannan bukatar ta taso. Domin tun ranar da aka yi haihuwar aka je aka dauki hotunan jariran don kai su ga sauran hukumomin da ke da ruwa da tsaki a wajen irin wannan bukatar.
Malam Lauwali da matar sa tare jinjiran su yan uku.
Source Leadership hausa
Title :
Wata Mata Ta Haifi ‘Ya’ya Uku A Kebbi
Description : Ranar Juma’ar da ta gabata ne wani magidanci mai suna Malam Muhammadu Lauwali, wanda aka fi sani da “Fura ke aiki” da ke zaune a Unguwar All...
Rating :
5