Assalamu alaikum. Malam idan mutum yana tukin mota ya buge mutane biu ko uku suka mutu cikin kure, ya zaiyi Azumin, kowane mutum sai ya yimai nashi ko sittin kawai zaiyi.
Daga Aboubakr Alkali.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Allah (SWT) yana cewa:
"DUK WANDA YA KASHE MUMINI BISA KUSKURE, TO ZAI 'YANTAR DA KUYANGA KO BAWA MUMINI, KUMA (ZAI BIYA) DIYYAH ZUWA GA IYALANSA (IYALAN WANDA AKA KASHE DIN) SAI DAI IDAN SUN YAFE".
Achan karshen ayar, Allah yace : "WANDA BAI SAMU BA (WATO WANDA BASHI DA BAWA, KO BAIWAR DA ZAI 'YANTAR) TO ZAI YI AZUMIN WATA BIYU (KWANA SITTIN) AJERE. DOMIN TUBA ZUWA GA ALLAH".
(Suratun Nisa'i, ayah ta 92).
Bisa wannan ne Malamai suka fahimci cewar duk wanda ya kashe sama da mutum guda, ko sun kai mutum 10 sai ka biya diyyar kowanne daga cikinsu, kuma sai kayi kaffarar 'yantar da baiwa ga kowanne rai guda da ka kashe. kuma idan kuma baka da ikon 'yantarwar, to zaka yi wannan azumi sittin din bisa kowanne rai.
Imam Ibnu Qudaamah (rah) yace:
"Duk Wanda yake da hannu acikin kisan kai sai ya yi kaffara, tare da dukkan wadanda suke da hannu acikin kisan. Kuma danginsa zasu hadu su biya diyyar rai.
Wannan shine ra'ayin mafiya rinjayen Malamai irin su Imam Hasanul Basary, da Ikrimatu, da Ibraheemun Nakha'iy, Sufyanuth Thawriy, Imam Malik, Shafi'iy, da kuma Mazhabin As'habur Ra'ayi.
– Aduba cikin ALMUGHNEE juzu'i na 12, shafi na 116.
Anan zamu fahimci cewar idan mutum goma suka kashe mutum guda, to kowannensu sai yayi kaffara, kuma zasu hadu ne su biya diyyar rai guda.
Amma Mazhabin Imam Shafi'iy da Hanbaliyyah (bisa wani Qaulin) sun ce idan mutum guda ya kashe rayuka masu yawa wadanda suka kai misali kamar mutum 30 ko 50 bisa kuskure, To zai biya diyyar kowannd mutum guda. amma idan yazo yin wasu daga cikin kaffarar, zai iya ciyarwa da muskinai maimakon azumin gaba daya mutane 50 din.
Amma kai tunda mutum uku ne, zakayi azumi 180 kenan da kuma diyyar dukkan mutum ukun nan.
Ina fatan Malam Abubakar ya fahimta.
WALLAHU A'ALAM.