Assalamu alaikum!
Da farko ina son miqa godiyata ga zauren nan, saboda ilimantar da mu ta hanyar addini da harkar rayuwar mu ta yau da kullum. Allah ya saka muku da alheri.
Don Allah ina so a fadakar da maza da mata akan hukuncin tura hotuna batsa da akeyi ta bbm ko watsapp. Sai ka ga aboki Yana tura wa abokin shi hotunan yan mata Wanda bai kamata ba. Basu da hira sai na matan banza, Idan ka duba ko sallah ba su maida hankali suyi ta balle addua ko karatun qura'ni
Nabiyu kuma, don Allah a taimaka mana da adduar da kuma hanyoyi da mata zasu shawo kan mazajen su masu neman matan banza.
Na uku, miye hunkuncin mijin da ke Neman tsohuwar budurwar shi, bayan dukanin su suna da aure. Dalilin sa saboda mahaifin yarinyar Yana riqe da babban muqami, wai yasan zai samu wani abu a wurin su, idan kuma matan shi ta sunnah tayi magana yayi mata zagi da gori wai bata da komai, har ya kai da Duka.
Nagode (pls a boye sunan sender din)
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Hakika duk mutumin da yake da sauran tsoron Allah azuciyarsa da kuma kwadayin samun lada alahirarsa ba zai shagaltar da kansa ko yaushe zuwa ga Ayyukan batsa ba.
Allah (SWT) yace ma Annabinsa (saww) :
"KA GAYA MA MUMINAI MAZA SU RINTSE IDANUWANSU, KUMA SU KIYAYE FARJOJINSU. WANNAN SHINE MAFI TSARKAKA GARESU. HAKIKA ALLAH MASANIN ABINDA SUKE AIKATAWA NE.
KUMA KA GAYA MA MUMINAI MATA SU RINTSE IDANUWANSU KUMA SU KIYAYE FARJOJINSU KUMA KAR SU RIKA BAYYANAR DA ADONSU SAI DAI ABINDA YA BAYYANA DAGA GARETA".
Idan mun duba wannan ayar, Allah yana magana da muminai ne. Don haka duk mumini mai imani bai kamata ya mayar da hankalinsa ga ayyukan batsa ba.
Kuma Ubangiji ya tsine ma masu kallon tsaraici, da kuma masu nuna tsaraicin nasu don a kalla.
* Duk matar da taga cewa mijinta yana aikata irin wadannan miyagun kallace-kallacen, abinda ya kamata ta fara yi masa shine wa'azi, nasiha, tare da jan hankalinsa.
Ta nuna masa cewa Shi fa amatsayin Shugabanta yake, kuma jagoranta aduniya da lahira. don haka yaji tsoron Allah, ya dena aikata abinda zai janyo masa matsala tsakaninsa da Ubangijinsa. tunda bai san ranar mutuwarsa ba.
Kuma Amatsayinki na matarsa, kema kina da dukkan abinda waccan 'Yar iskar take nuna masa.. Don haka ki rika gyara jikinki, ki chanza kwalliya, ki yawaita fesa turare don jan hankalinsa.
Ki chanza dabi'un zamanki dashi. Ki zama mai tarairayarsa ako yaushe, mai faranta masa rai da kyawawan kalamai. Kuma ki yawaita addu'a domin neman zaman lafiyarku dashi ya dore.
Na san akwai matan aure acikin Zauren nan. ba zasu rasa shawarwarin da zasu baki ba.
Allah ya rufa asiri.
WALLAHU A'ALAM.