Asslamu alaikum. Malam wai dole ne Idan macce zatayi wanka bayan ta gama jinin al'ada sai ta tsefe kanta?
Kuma Idan jini ya daukewa macce da misalin karfe 5 ko 6 sallar la'asar kawai zatayi ko har da azahar?
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah.
Ya danganta da irin kitson da yake kanta. idan kitson ba mai tsanani bane, kuma an yishi yadda ruwa zai iya ratsa cikinsa sosai har zuwa jikin fatar kanta, to wannan ba sai ta tsefeshi ba, Idan zatayi wankan Haila ko janaba.
Amma idan kitson ya zamto mai tsanani sosai, ko kuma an sanya igiyoyin roba an daure kitson, to WAJIBI NE atsefe irin wannan kitson domin ruwa ya samu damar ratsa cikin gashin kanki.
Idan jininki na haila ya dauke kafin faduwar rana da Minti goma ko sha-biyar, ko fiye da haka, to wajibi ne sai kin yi Sallar Azahar da la'asar bayan kinyi wanka.
Amma idan ya dauke daf da faduwar rana, kamar minti 4 ko 5 ko Qasa da haka, to la'asar kadai zaki yi bayan kin yi wanka.
Haka abin yake dangane da Sallolin Magriba da Isha'i idan jininta ya dauke kafin fitowar alfijir.
Idan mintunan tsakanin daukewar jinin da kuma fitowar Alfijir, in dai mintunan sun kai a sallaci raka'o'i biyar ko sama da haka, to zaki sallaci Magriba da isha'i.
Amma idan mintunan basu fi asallaci Raka'a uku zuwa Qasa ba, Magriba kadai zaki rama.
Duk matar da take tsammanin Daukewar jininta acikin wani yini, to WAJIBI ne gareta ta rika dubawa daf da faduwar rana, taga ko ya dauke. Don gudun kar ya zamto tayi sakaci da sallolinta.
Hakanan idan cikin dare har zuwa daf da fitowar alfijir. shima wajibi ne ta rika dubawa.
WALLAHU A'ALAM