TAMBAYA TA 1598
*******************
Assalamu Alaikum. Dafatan Malam yana lafiya. Malam ina da tambayoyi kamar haka:
1. Malam ya halatta idan mutum na sallah wani yazo yana neman shi kuma bai san yana sallar ba yayi mashi gyaran murya don ankarar da shi cewa sallah yake?.
2. Malam a cikin arba'una hadith akwai hadisin daya bayyana yadda ake halittar mutum har yace ana aikowa mutum mala'ika ya busa masa rai kuma ya umarce shi da kalmomi hudu, arzikinsa, ajalinsa, ayyukansa, tababbene ko mai rabo. To mlm duk da banji a nassi ba amma naji wasu mutane na cewa mutum na rubuta dukkan abinda zaiyi a duniya kafin ahaife shi, to mlm wannan baya cin karo da wancan hadisin ko duk daya ne? Kuma menene halaccin waccan maganar a musulunci?
Daga S. B Aliyu Mahuta
AMSA
******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Ko acikin litattafan Fiqhu, malamai sun nuna halaccin yin hakan. Sallar mutum bata baci ba. Sai dai kuma idan abun yayi yawa zai iya janyo masa zubewar ladansa saboda ita sallah ibada ce wacce ake so mutum ya shagaltu da zallar tsoron Allah acikinta. Kuma Allah ba ya karbar sallar da babu tsoron Allah acikinta.
2. Abinda hadisi ya tabbatar mana shine Mala'ikan ne yake rubuta wadannan abubuwan abisa umurni daga Allah (SWT) Amma ba jaririn ne yake rubutawa ba.
Wanda kuma ya fadi sabanin haka, dan yayi ne da kuskure, to muna kyautata zaton Allah zai gafarta masa. Amma idan da gangan ne ya juyar da zancen Manzon Allah (saww) to ana tsorace masa kafirci. Kamar yadda Allah yake fada acikin Alqur'aninsa.
WALLAHU A'ALAM.