TAMBAYA TA 1608
*******************
Assalamu alaikum, malam dan Allah kayi hakuri da mu kada ka gaji damu, don babu abinda zamu ce maka sai dai Allah ya saka maka da AL-KHAIRI
Malam ina neman fatawa ne akan bawa ko baiwa. shin ya ake mallakan bayi ne a wannan zamani? domin naga wannan zamani ba a yaki kamar da lokaci ANNABAWA DA SAHABBAI, dan naji ance sarakuna suna da bayi, shin ana sayen bayin ne a kasuwa, ko kuma su bayin ne suke zuwa da kansu gun tsarakuna?
BAYAN HAKA kuma a wajajen mu wasu suna cewa wai makada ( masu buga kalangu) da wanzammai da masu Qira ance wai bayi ne su, dan hakane ma ba a cika basu diya aure ba, kuma ba a cika aura daga garesu ba, DAN ALLAH HAKA NE? Daga wani bawan Allah.
AMSA
******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah.
Hakika a Musulunci ana Mallakar bayi ne ta hanyoyi kamar haka:
1. Ganimar yaki: idan akayi yaki tsakanin Muminai da kafirai, kuma aka samu nasara akan kafiran to dukkan matayensu da 'ya'yansu da dukiyoyinsu sun zama Ganimar yaki. Har ma sauran mayakan da ba'a kashe ba. Sun zama bayi. Za'a rarrbasu tsakanin Sojojin Musulmai wadanda suka halarci wannan yakin.
2. SAYE: Awancan zamanin akwai kasuwanni da kuma 'yan kasuwa wadanda suka kebantu da saye da sayarwar bayi da kuyangi. Zaka iya zuwa kasuwa wajensu ka duba, ka zabo bayi ko kuyangi ka sayo ka kawo gidanka.
3. GADO: Idan Mahaifinka ko Mahaifiyarka ko kuma wani wanda kake da gadonsa ya mutu ya bar bayi ko kuyangi, to su ma za'a rabasu ne gwargwadon yadda rabon gadon ya kama. Don haka kenan zaka iya mallakar bawa ta hanyar gado.
4. HAIHUWA: Idan ka hada aure tsakanin bawanka da baiwarka, ko kuma ka hadata da bawan wani, Duk 'ya'yan da baiwarka ta haifa to su ma duk bayinka ne.
5. KYAUTA: Wani daga cikin makusantanka zai iya baka kyautar bawa ko baiwa.
Amma idan kayi SA-'DAKA da kuyanga (wato saduwa da ita) har ta haifa maka zuriyya, to su wadannan ba bayi bane agareka. Suna da dukkan 'yanci kamar yadda adda sauran 'ya'yanka suke dashi.
EH DA GASKE NE Har yanzu akwai bayi agidajen Sarakuna da Manyan Malamai. To amma fa kusan mafiya yawansu sun mallakesu ne ta hanyar Gado daga wajen iyayensu.
Amma har yanzu akwai rahotannin da suke nuna cewar ana samun cinikin bayi a wasu kasashen Africa ta Arewa (kamar su Mauritania, Tunisia, Algeria da Morocco). Da kuma wasu kasashen irin su Nepal, India, Burma, China, da sauransu..
Dangane da wanzamai, Makera, Mahauta da saura su, Ni awajena babu wata hujjar da take nuna cewa asalinsu bayi ne. Sai dai na san cewa sana'a suke gudanarwa wacce take taimako sosai acikin al'ummah.
WALLAHU A'ALAM.