A kwanan baya ne rundunar tsaron sojin Najeria a wani yunkuri da suka yi na neman ceto 'yan matan nan da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace daga makarantar kwana a gari Cibok ne suka yi nasarar kubutar da wasu mata da 'yan kungiyar suka tsare.
Rahotanni dai sun nuna cewar sojojin sun canza wa wadannan mata da wurin zama daga sansanin da suke ko kokuma inda aka ajiye su da farko wanda hakan ya kawo cecekuce da tofa albarkacin baki daga mutane, har ma wasu na tunanin wadannan mata ka iya bada labarun sirri ga 'yan kungiyar musamman bisa zargin cewar wasu daga ciki mtan 'yan kungiyar ne.
A wata hira da ma'aikacin sashin Hausa yayi da Muhammad Kanar shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA. ya bayyana cewar maganar canza masu wurin lallai haka ne, to amma yadda ake fahimtar abin ya sha ban-ban da abin da ke guda na. saboda idan mutum ya sami kansa cikin wani mawuyacin hali na tsangwama ko hadari da suka shiga, to lallai akwai matsalar kalubalen tsangwama daga jama'a.
Dan haka akwai wani shiri wanda ya ke taimakawa irin wadannan jama'a domin maida su cikin hayyacin su. akwai sanannu kuma kwararrun da aka kai wadannan mata wajan su domin samun taimako.
Daga karshe yayi karin bayanin cewa duk maganganun da jama'a ke yi dangane da cewar wadannan mata suna bada bayanan sirri ga 'yan kungiyar ba gaskiya bane. domin kuwa tun daga ran da aka kawo su, basu rabuwa da 'yan jarida, ma'aikata da sauran su kuma babu wanda zai ce ga zahiri ko shaidar cewa an sami tabbacin hakan.
Title :
Sojoji Sun Canza Wa Matan Da Suka Ceto Wurin Zama
Description : A kwanan baya ne rundunar tsaron sojin Najeria a wani yunkuri da suka yi na neman ceto 'yan matan nan da 'yan kungiyar Boko Haram su...
Rating :
5