Kalmar "Fatalwa" wani abu ne wanda ba bako bane a kunnen duk wanda yake zauren nan. saboda yawaitar yadda tsofaffi da iyaye mata suke yawan bada labarai ko tatsuniyoyin da suka shafi FATALWA.
To shin da gaske ne akwai FATALWA??
AMSA: Eh gaskiya ne akwai FATALWA. Amma Malamai sunyi bayanai masu dama akan ta. Mafiya rinjaye daga cikinsu sunce Ita fatalwa wani nau'in Aljanu ne wadanda suka shahara sosai wajen GUDANAR DA SIHIRI DA TSAFI irin nasu na Aljanu.
Mafiya yawa daga cikin fatalwa suna Kashe duk Mutumin da suka hadu dashi. Wani lokacin ma FATALWA ta kan cinye naman jikin mutum 'danye... (kamar yadda yazo acikin AAKAMUL-MARJAAN).