Mutane da yawa sun sha yi min irin wannan tambayar idan mun hadu dasu. Saboda yana daga cikin batutuwan da suka shige musu duhu.
To ga amsar kamar haka:
* EH Aljanu suna mutuwa. Hujjah kuwa ita ce ayar nan wacce Allah yake cewa : "DUKKANIN WANI RAI SAI YA DANDANI MUTUWA".
To tunda su ma rai ne dasu, ashe kenan su ma zasu dandaneta.
Dangane da Addu'ar da Iblees yayi wacce ya roki Allah cewa a jinkirta masa har zuwa ranar Alkiyamah, eh hakane. Kuma Allah ya amshi rokon nasa.
Sai dai kuma wannan lumanar bata game dukkanin Aljanu ba. Sai dai dangin shi Iblees din daga cikin Aljanun.
Malamai sunyi maganganu masu tsawo akan Mas'aloli irin wadannan. kamar yadda Abu Abdillah Ash-Shibliy ya kawo acikin Mashahurin Littafinsa.
Kuma koda azamanin Magabata na kwarai an samu da dama wadanda tsautsayi ko kuma wani dalilin yasa sun kashe Aljani.
Sayyidah A'ISHA ma har diyyah ta taba biya bisa wani aljanin da ta kashe bisa rashin sani.
In sha Allahu nan gaba zan kawo yadda abin ya faru.