Watarana wani saurayine suna hira da budurwarsa,sai yake cemata gobe kuwa zan miki kyauta da zai baki mamaki matuka, taji dadi sosai dan tun awurin tafara masa godiya
washe gari ta tara kawayenta take gaya musu cewa, yau abin alfaharita zai mata kyautarda be tabamata irintaba,shiyasa ta tarasu dan su tayata murna
can taga ya dade be zoba,saita yanke shawarar bara ta kirashi taji ko lafiya? Tana kira tace hello sweetyna najika shiru lafiya de ko? Yace mata karki damu my heart ganinan nakusan zuwa
saitaji wani dadi, baa jimaba sai gashi da wata bakar leda yanata murmushi, ya iso wurin da suke, bayan sun gama gaisawa da kawayen nata, itako mutuniyan harta tsagu taga menene acikin ledar
kawai sayya mika mata, tana budewa saitaga buredi me yanka yanka, ranta ya baci kawai saita kasheshi da mari,tace
amma ka rainamin wayo, kan wannan banzan buredin kaketa karanta cewa zakayimin kyauta, Allah ya wadaran
kawai saita wurga masa ledan, kafin ledar ta fado saiga makullin sabuwar mota kiran KIA Ya fado
tofa IN KAINE YA ZAKAYI?
KO
IN KECE YA ZAKIYI?