Lugudan wutan an zafafa shi ne cikin dare a birnin Sana'a fadar gwamnatin kasar ta Yemen da nufin afkawa wasu dakaru da ke mara baya ga tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh
Wannan dai na zama farmaki na farko da ya afkawa birnin tun bayan tsagaita wuta na tsawon kwanaki biyar, koda yake ko da a jiya Litinin sojojin sun fara ayyukansu a arewacin lardin Saada da kudancin birnin Aden. Inda saudiyya ta yi ta cilla bama-bamai don rusa tashoshin jiragen ruwa da na sama.
Wannan yarjejeniyar tsagaita wuta dai ta gaza dorewa duk da irin kiran da MDD ta yi, na a bada karin dama wajen kai kayan agaji ga dubban mutane da ke cikin matsananciyar bukata, ta abinci da magunguna a wannan kasa da ke da mutane miliyan 25, kana daya daga cikin mafi talauci a tsakanin kasashen Larabawa.
Kasar Saudiyya dai da kawayenta 'yan Sunni, sun kaddamar da aikin hadin gwiwa kan fatattakar mayakan na Houthi da ke zama 'yan Shi'a masu samun tallafin kasar Iran, inda yanzu farmakin na Saudiyya ya kai tsawon makonni bakwai, a kokarin da suke na sake maida shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi wanda dan Sunni ne kan karagar mulkinsa.
Title :
Saudiyya ta koma luguden wuta a Yamen
Description : Lugudan wutan an zafafa shi ne cikin dare a birnin Sana'a fadar gwamnatin kasar ta Yemen da nufin afkawa wasu dakaru da ke mara baya ga ...
Rating :
5