TAMBAYA TA 1607
********************
Assalamu alaikum malam allah yakara basira ya jikan iyayenmu amin. Malam tambayata itace mutum ne yake sana'ar siyar da jakuna da dokuna sai naji wasu suna cewa ta haramta idan yaci kudin kamar yaci ne shine nake neman karin haske akai malam Allah yabiya mana bukatummu. Nagode.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah.
Hakika ya halatta ga Musulmi yayi sana'ar siyar da jakkai (jakuna) da dawakai. wannan Halastacciyar sana'a ce tun zamanin farko.
Tarihi ya nuna cewa Manzon Allah (saww) da kansa ya kan tura kasuwa aje a sayo masa Doki. Hakanan Sahabbai da dama sunyi sana'ar sayen doki da siyar dashi domin samun riba kamar na kowanne kasuwanci.
Hakanan shima jaki zaka iya saye ka sayar. Tunda dai mu anan Qasar arewacin Nigeria ana amfani da Jaki domin yin tafiye tafiye da kuma daukar kaya zuwa wasu guraren.
Amma kamar Kafiran da suke zuwa daga Kudancin Qasar nan suna sayen Jakkai domin yankawa suci, bai halatta musulmi ya zama dillalinsu, ko kuma mahaucinsu ba. Domin addininmu ya haramta mana muyi taimako wajen aikata sa'bon Allah. (aduba ayah ta 3 acikin suratul Ma'idah).
Misali kaga sayar da dawa da gero da dabino duk halastattun kasuwanci ne. Amma duk da haka bai halatta musulmi ya zama dillalin gidan giya, yana saya musu dawa ko gero ko inabi ko dabino domin suje suyi giya ko barasa dashi ba.
WALLAHU A'ALAM.