Kungiyar Real Madrid ta sallami kocinta Carlo Ancelotti, bayan da ya yi shekaru biyu yana jan ragamarta.Kociyan, dan kasar Italiya mai shekaru 55 ya dauki kofin Spaniya da kuma Kofin Zakarun Turai kuma na 10 da Madrid ta lashe jumulla.Sai dai kuma a kakar wasan bana Madrid ba ta dauki kofi ba, yayin da Juventus ta cire ta daga Gasar cin Kofin Zakarun Turai, sannan Barcelona ta dauki kofin La Ligar bana.Madrid din ta kare a mataki na biyu a teburin La Ligar bana da tazarar maki biyu da Barcelona ta bata wacce za ta buga wasan karshe na kofin Spaniya da Kofin Zakarun Turai.
Shugaban Madrid Florentino Perez ya ce sun shiga tsaka mai wuya kan yanke wannan hukuncin, amma sun yabawa Ancelotti da gudunmawar da ya bai wa kungiyar.Haka kuma shugaban ya ce nan ba da dadewa ba za su sanar da sunan sabon koci da za su dauka wanda zai horar da Madrid.Ana hasashen cewar Rafael Benitez ne zai maye gurbinsa, yayin da wasu ke cewa kociyan Borussia Dortmund Jurgen Klopp ne zai dawo horar da Madrid din.
Title :
Real Madrid ta kori Carlo Ancelotti
Description : Kungiyar Real Madrid ta sallami kocinta Carlo Ancelotti, bayan da ya yi shekaru biyu yana jan ragamarta.Kociyan, dan kasar Italiya m...
Rating :
5