TAMBAYA TA 1610
*********************
Assalamu Alaikum
Ina fatan Mallam yana lfy. Allah ya saka da alkhairi. Mallam ya'r uwata ce tayi min tambaya cewa:-
Suna tare da mijinta duk irin yadda ya sadu da ita bata ta6a samun wani jin dadi irin na saduwar miji da mata ba.
Shine muke so a taimaka mana da abin da ya kamata muyi. Allah ya saka da alkhairi.
Daga wani bawan Allah.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah. Hakika ita wannan matsalar tana da Musabbabai da dama, kala-kala.
Kamar yadda nayi bayani kwanakin baya, akwai wadanda Ciwon sanyi ko Basur, sukan haddasa musu wannan matsalar.
Akwai kuma Wadanda sukan hadu da Matsalar ta sanadiyyar cututtukan da ake dauka ta hanyar jima'i. Kuma akwai wadanda Shafar Aljanun JINNUL ASHIQ.
Rashin tsaftace al'aura, da kuma sanya sabulu ko kuma wani abu mai kunshe da zafafan sinadarai shima yana kawowa rashin jin dandanon jima'i ga mace.
Abinda ya kamata kuyi shine ku binciki kanku. Idan har akwai wasu daga cikin dalilan nan dana lissafa, to da zarar kun magance tushen faruwar abin zaku ga Qarshen matsalar yazo. da mutane yardar Allah.
Amma akwai wani magani mai suna MUMTAZ daga ZAUREN FIQHU. An hadashi da sinadarai guda shida don magance matsaloli kamar haka:
1. Budewar Gaban mace.
2. Kurajen gaba.
3. Kaikayin Gaba.
4. Rashin jin dandanon jima'i.
5. Bushewar gaba (daukewar ni'ima).
Ana yin matsi dashi sai bayan kamar awa 1 sai aje awankeshi da ruwan dumi. In sha Allah yana Matsewa al'aurar mace kuma yana magance matsalar Kurajen gaba, kuma yana Qara nishadi yayin saduwar aure.
Inq ganin ku nemeshi daga ZAUREN FIQHU ko kuma wani waje mafi kusa daku. in sha Allah za'a dace.
WALLAHU A'ALAM.