Shugaban hukumar kwallon ta duniya-Fifa Sepp Blatter, na ci gaba da fuskantar matsin-lamba lallai sai ya sauka daga mukaminsa, sakamakon zargin cin-hancin da ake yi wa wasu manyan jami'an hukumar.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta tarayyar Turai, Uefa, Michel Platini da kuma Firayi Ministan Biritaniya, David Cameron su ma sun bukaci Sepp Blatter ya yi murabus.
Sai dai yayin da suke wadannan kiraye-kirayen, Sepp Blatter na samu goyon bayan daga wasu kasashe, ciki har da Rasha, hasali ma, shugaban Rasha Vlamir Putin ya ce binciken da Amurka ke yi ma wani rabewa ake da guzuma don a harbi karsana.
Saboda a cewarsa ana nema ne a hana kasar karbar bakuncin gasar kofin duniya a shakara 2018, alhali ba su da hurumin binciken lamarin:
A bangare guda kuma, kasar Afirka ta kudu ta musanta zargin cewa ta ba da cin-hanci kafin ta samu damar karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da aka yi a kasar a shekara ta 2010.
Title :
Platini ya bukaci Blatter ya yi murabus
Description : Shugaban hukumar kwallon ta duniya-Fifa Sepp Blatter, na ci gaba da fuskantar matsin-lamba lallai sai ya sauka daga mukaminsa, sakamakon zar...
Rating :
5