TAMBAYA TA 1601
******************
Aslm Alkm. ALLAH ya saka ma malam da alkhairi ga gudunmawar da kake baiwa muslunci. Malam ataimaka a amsa min tambayata d neman addu'ar yan uwa musulmi akan halinda nake ciki. shekaruna 27 aduk time din da wani yazo neman aurena matukar ya Nace zanji bana sonsa wlh, idan na fara son wani kuma idan nai masa maganar auran sai injisu shiru, akan haka mahaifiyata tace man inje gidan wata mai bada maganin gargajiya, matar aljani ne ke xuwa kanta kai masa bayanin matsalarka sai yayi addu'ah ya tofa aruwa yace mutum yasha ya shafa afuska, bayan nan kuma in baiwa yara sadakar kosai da waina akan ALLAH ya yayewa mutum damuwar sa shikenan. tambayata anan hakan ya halasta don gudun fadawa shirka. sannan ina neman addu'ar yan uwa musulmai da bakunansu masu albarka akan ALLAH ya yaye man wannan matsalar ya kawo min mijin aure na kwarai don ALLAI aboye sunana.
(Daga wata Baiwar Allah).
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah.
Hakika Allah shine ya halicci mutum da Aljan domin su bauta masa. ba don su rika zaluntar juna, ko kuma dulmiyar da juna acikin shirka da kafirci ba.
Kuma Allah shine wanda ya halicci dukkan bayinsa, kuma ya halicci dukkan ayyukansu, kuma ya Qaddara dukkan abinda zasu samu da kuma abinda zai samesu tun gabannin zuwansu duniyar nan.
Baiwar Allah amatsayinki na Musulma kuma Wacce take da ilimin addini da hangen nesa, tabbas kinyi tunani sosai da kika nemi wannan fatawa. Saboda irn wannan abun yana nan da yawa acikin unguwanni da kauyuka da birane.
Yawancin wadannan matayen da suke bada magani ta hanyar samun taimakawar Aljanu, su kansu majinyata ne wadanda Already dama akwai aljanu ajikinsu. bayan Aljanun sun zauna tare dasu, zasu bukaci cewa ita wannan marar lafiyar ta rika yi musu wani yanka ko sadakar wabi abu, abisa wasu kayyadaddun lokuta. idan tana yin haka su kuma zasu taimaka mata ta rika bayar da magani.
Shi kuma Aljanin zai kasance tare da ita. idan Mutane sun taho wajenta, tun kafin su Qaraso shi wannan aljanin zai zo ya bata labarinsu.
Idan sun zo kuma, shi zai zo ya bayyana akanta. Yana da'awar sanin gaibu, yana fadar kalamai kamar irin nasu na bokaye da 'yan duba.
Zai iya gaya miki tarihin rayuwarki, harma da abubuwan da suke damunki ayanzu. wannan zai sanya nan da nan zuciyarki tayi Imani da lamarinsa.
Don haka su kansu irin wadannan mutanen BOKAYE NE irin wadanda Allah da manzonsa ya umurcemu mu nisancesu.
Duk wannan abun ba daidai bane. Hatta sadakar da zasu ce kiyi. tana kunshe da wasu tarnakaki masu hadari ga imaninki.
Amatsayinki na musulma Mumina Ki nisanci irin wadannan abubuwa. Ki rike ALQUR'ANI da Sunnar Annabin Rahama (saww) duk abinda Alqur'ani bai yi miki ba, to tabbas irin wadannan mutane ba zasu iya yi ba.
'Yan uwa ku taimaka mata da addu'a. Tabbas wannan baiwar Allah mutuniyar kirki ce. Ni na santa, kuma na san mahaifinta. Mahaifinta Malami ne. kuma ya san mutuncin mutane.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM.