Assalamu alaikum, mallam gaisuwa da fatan alkhairai. Tambaya ta ita ce:
mallam aure nake nema ga wacce takeyin iddah shin ya halatta na sanar da mahaifiyarta cewar ina neman yar'ta da aure?
AMSA
******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
A'a kar ka gaya ma Mahaifiyarta. domin kuwa zata sanar mata. Kuma Allah ya hana bayyanar da neman auren Matar da take cikin Iddah.
Abinda ya halatta agareka shine irin zancen nan da ake cewa "JIRWAYE DA KAMAR WANKA". Misali kamar kace : "Wance ai mutane da yawa suna son su samu Mace Irin ki su aura".
Sannan kuma ba kiwacce mai iddah bace ake yi ma irin wannan zancen. Sai wacce Babu sauran wata igiyar aure tsakaninta da Mijinta. Misali kamar wacce Mijinta yayi mata saki daban daban.
Amma in dai saki daya yayi mata ko biyu, to kaga har yanzu yana da sauran iko akanta. zai iya mayar da ita aduk lokacin da suka daidaita suka yi Sulhu. Don haka bai halatta ka kulata ko ta wacce irin hanya ne. ballantana har ka sanar da Mahaifiyarta ko Qawarta. wannan duk bai halatta ba.
WALLAHU A'ALAM.