SAUDA DAMA IDAN SHAKIRA Talura da irin rayuwarta wadda takoma cikin soyayya lokaci guda sai abin yabata mamaki babban abindayake daure mata kaima shine soyayyar dantala dakoda yaushe take dada girma acikin zuciyarta kamar wacce ake zuba mata taki.
Idan harta baro wajen su na aiki to har Allah Allah take washe gari tayi yamma takaraso domin suje wajensu kawai taganshi sannan kawai zataji sanyi aranta tawani bangaren kuma tana tausayin rayuwarta yadda zata kasance ganincewarma kotana son maso wanine.
Saidai abindayafi karfafa ,mata guywa shine tasoshi din tunda dai iya i,maninta azuciyarta tbbs dantala mutumin kirkine danhaka takara bawa sonsa dama yaketa cikin zuciyarta inda ya shiga harma yasamu gurin zama darandam.
Wannan sune irin yawan tunanikan da shakira taketa fama dasu kodayaushe babban burinta kuwa baiwuce ace yau dan tala yafirtamata cewa yana sontaba tbbs da ranar zatay farin cikin dabata tabayiba arayuwarta.
Yauma kamar kullum su shakiran sunzo gurin 'yan aikin abindaya faru jiya shiya faru yau danhaka ba asamu wani dan canjin lamariba saida wani abu daya daurewa dantala kai shine tunda sukai sallar la asar yanemi sale yarasa yai kokarin buga masa waya amma kuma akashe danhaka dole dasuka raba kudin sallamarsu shiya karbar masa sannan yazauna agurin danyasan sale dakudi dukma inda yatafi to saiya zo yakarbi kudinsa.
*******
kai zahra nidai nagaji da wannan lamarin wlh gskya da ace da hali da saina furtama dantala cewa inasonsa wlh kawai ninasan halin danake ciki danni gsky zahra ina azabtuwa wlh.
Shakita ce tay wannan furucin lokacin da suka baro gurin su dantalan.
Kafadarta zahra ta dafa sannan tamaida hankalinta kan tukin datake tace.
Shakira abinda duk hakuri bai kawoshiba rashin hakuri mafa bazai kawoshiba karfa kimanta yau kwana uku kenan dake da dantala dakukasan juna wadda akalla muda mudaina zuwa gunnan sai bayan nan da kwana hudu.
Shakira kiyi hakuri inason koda kunfara soyayyane yasan yafara soyayya da nagartacciyar mace ba wacce yasameta asadakaba dan haka Dan Allah karki bani kunya kidaure kihadiye maitarki kizubamin ido kawai.
Shakiran bata kara cewa komaiba harsukazo kofar gidansu shakiran sannan tasauketa inda shakiran tace yabazaki shigoba.
Zahra tace sauri nakeyine dan ummanna taymin magana zata aiketa wani gun.
Sukai sallama sannan shakiran tanufo gida.
'yan mata dan Allah idan bazaki damuba zanso nai magana dake.
Dasauri shakiran tajuya dan batama lura da awai mutum agefensuba yayinda zahra tasauketa daga mota.
Wani katon three quarter yasaka duk yayi datti sai wata riga data dan damemasa jiki yadebi hannayensa biyu duk yacusa amanyan aljihunan.
Shakira takalli mai maganar ahankali.
Badan atsaye yakeba sannan acikin nutsuwa sosai da zata iya tsammanin ko yasamu tabuwane.
Cikin karfin hali takarasa dan kusa dashi sannan tace malam lpy kake son magana dani?
Ya akai kasanni harka tsaya aguna?
Saurayin yadanyi murmushi har dan jan hakwaransa suka fito sannan yadubi shakira yace.
Sunana sale ni babban abokin dantala ne nazone gurinki tareda sako wanda abokina ya aikoni dashi.
Acancikin zuciyar shakira wani farin cikine ya lullubeta dan tasan zai wahala ba sakon data dade tana marmarin zuwansabane agareta.
Amma azahiri kuma fuskrta babu abinda ta nuna sanna ta dubi salen tace.
To inajinka mallam fadamin wanne sako yabaka kabani.
Sannan salen yafara.
Wato azahairin gsky shine kafin kwana uku dasuka wuce abokina dantala mutum ne mai yin komai cikin nutsuwarsa sannan bashida damuwa kokadan, mutum ne kodayaushe yake acikin nutsuwarsa amma kuma kwana uku dasuka wuce kwata kwata yacanza tunaninsa yajuya izuwa tuananin wani abu guda daya sannan nutsuwarsa itama tajuya izuwa tunanin wannan abin guda daya wato atakaicedai gabaya bayyanar wannan abin yajuya akalar rayuwarsa.
Wannan abun kuma ba komai bane face ke SHAKIRA wadda alokacin dana nutsa da nazari da bincikensa saiyafadamin cewa yakamu da matukar sonki wadda inhar son dayake miki kuma bai mallakekiba to tbbs rayuwarsa tana ciki aminci.
Gadayansu sukai murmushi na lokacin sannan salen yace toshikenan godiya marar adadi shakira hakika bani da abinda zan saka miki saidai nace Allah yasaka da Alkairi.
Shakira tace hakane amma mukarasa cikin gidanmu mana kodan lemo kasha amatsayinka na babban bako.
Duk da cewa rabonsa dayasha lemon yamanta amma saiyai murmushi yacemata a a kibarshi bakomai bana bukatar komai tunda har bukar danazo nasameta.
Sunyi sallama cikin mutunci da aminci inda kowa daga cikin su yarabu da matukar farin ciki bisa nasarar bukatarsa.
Afuwa zancigaba gobe.
Yi comment dan nuna ra ayinku Pls..
Admin M. Kabiru Muhammad