LOKACIN DA DANTALA yaji kalaman dasuka fito daga bakin saleh saigabadaya jikinsa yai sanyi sannan yay tunani yaga cewa duk inda masoyi yake tbbs sale yakai agareshi sannan maye amfaninma ace suna zaman amince dayarda da juna amma kuma zai boye masa sirrinsa danhaka saiyajuyo yadubi sale yace.
Sale agsky dabanyi niyyar fadamaka komaiba amma ayanzu tunda harka hadani da girman Allah to tabbs kagama dani kamar yadda kafadamin jiya tbbs nakamu dason wannan yarinyar datazo jiya muna aiki amma nasan kuma abanza tunda niba kowabane danhaka nasan nasakaina acikin bala ine kawai sabida haka wannan shine abindayake damuna ina fatan yanzu ka gamsu.
Maimakon sale yai magana saiya tuntsire da dariya sannan yace inbanda abinka dantala kaida kake da farinjini haka harkuma kake tsoran tarar wata yarinyar kafurtamata kalmar so bayan karkamantafa sauda dama agabana yan matan sunkawo kansu gunka suna furtamaka kalmar so.
Amma shikenan dantala karkadamu wlh wannan karamar matsalace nasan kai bazaka iya samunta kafada mataba sabida kana ganin kamar tafi karfinka
danhaka kabar komai ahannuna nizan isar maka dasakonka agareta wannan shine taimakon dazan iyayimaka amatsayinka na babban abokina.
Dasauri dantalan yakalleshi yace.
A a...a a sale banason kajawomin wulakanci dacin zarafi haka kawai ina zaune cikin mutuncina kaje kasa yarinya tawulakantani danhaka babu ruwanka kabarni daciwon dake damuna zan roki Allah yaciremin sonta azuciyata.
Dantala! Salen yai kiransa yace na am.
Sannan yace wlh Allah yarinyarnan tanasonka danhaka kataymaka kabarni naje nasanar maka sakonka ninayarda duk wani wulakanci dazataymin sannan taymaka nizan daukesu.
Dantala yagirgiza kai yadubi sale yace haka kace.
Sale yace hakanace.
Yace ok duk abindaya biyo bayadai kaikasiya.
-----------------
idan da akwai wani wanka da kwalliya dashakira takeyi aduniya yayi mata kyan dabai taba yimataba tofa saidai wankan birthday dinta wanda takeyi duk shekara wanda idan kaganta lokacin datadau wankan taikwalliya takece raini tofa ko hasidin izahasada ne kai saika sallamata.
Amma wai sabida zataje wajen 'yan aiki taga hasken farin watanta tayi wanda yafishi ayau idanka hada wankan birthday dinta dana yau tbbs nayau yayi masa fintinkau ita kanta ummanta saida ta tambayeta komaye dalilin haka.
Cemata tai kawai yau jin dadin duniyarta take kamar ranar birthday dinta murmushi mahaifiyarta ta taimata kawai tasaka mata albarka sannan suka jere dazara suka tafi gurin yan aiki.
Ahanyarne zara take fada mata shakira kikulafa karki yadda kizubarmana da aji plss idan dahalima banaso ko kallonsa kiyi danhakanma zai iya jawo matsala.
Karkidamu kawata insha Allahu bazan baki kunyaba shakirantace.
Sannan azuciyarta kuma takecewa tab tayama za ai naje gunnan ban kalli dantalaba haba zahra ai gwarama banyi tapiyarba kenan.
Sun isagun sun samesu kamar yadda suka samesu jiya saidai yau gaba dayansu akasa suke sabida tuni biyar tawuce batareda bata lokaciba shakiran tabawa dantala kudin kamar jiya inbanda satar kallo dasuke wa junansu babu wanda ya iya furta wata kalma har shakira da zahran suka juya suka shiga mota suka tafi.
Hankalin dantala yadan tashi yamika kudin ga danjuma sannan yajawo sale yacakumi rigarsa gefe inda baza aji abinda zasu fadaba sannan yace.
Wannan ai wulakancine haba sale yazakaimin haka kaida kace zaka isarmin dasakona amma kuma gashinan hartazo tajuya komotsi kakasayi sannan karka mantafa kayi rantsuwa da Allah zaka taimakamin kuma danme hartazonan bakace matakomaiba.
Maimakon salen yace wani abu saiya tuntsire da dariya harda dan faduwa kasa sannan yatashi ya karkade rigarsa yace au.. Dama kanaso nagayamata kenan ainazata danaji kace komai najawo kaina nikadai nayi tsammanin abin baidamekaba.
Sai alokacin dantala yaji kunya tbbs yasan yafadama dantala haka dazu dazasu fito to amma dole yayi hakuri tunda giyarsoce yanxu tadebeshi.
Kafin dantalan yakara cewa komai sai sale yace kaga karka damu.
Dama hadin kanka nakeso nasamu sabida haka nayi rantsuwa da Allah insha Allah gobe iya nzu sakon soyayyarka yadade da zuwa zuciyar wannan kyakykyawar yarinyar sannan daga yau kabani assignment zan nemomaka gidansu sunanta dama dai sauran bayanai danhaka karka damu kaidai kabani 25 hours.
Yakarasa maganar yana dariya saikace wani tababbe.
Dantala yayi murmushi sannan yace toshikenan inaimaka fatan samun nasara.
Tun amotar shira yakarke tsakanin 'yanmatan inda zahra tadubi shakiran tace haba shakira wlh kinkusa bada mata kinga yadda kike yawan kallonsa kuwa ke ko kunyama bakyaji mtss..
Kinga zahra nifa dannaganshi kawai naje barina fadamiki zahra dazan kwana inakallon fiskar dantala ma abociyar haske wacce kodayaushe take acikin murmushi wlh bazan gajiba.
Zahra tai murmushi tace amma kinga da alamun nasara acikin al amuranmu dan kinga yadda yake kallonki kuwa kedai bari saima goben..,..