SHAKIRA Tadubi zara tace kunya kuma zara toya zakiyi tunda mahaifinkine ya turaki ai dole ki biyayya.
Tadan yamutse fuska to shikenan nidai shirya kirakani dan Allah dan gaskiya bazan iya zuwa gurinnan nikadaibafa dan akalla mazane fa agurin sunfi su talatin kuma ni kinsan babu abinda yake yawan sakani razani kokuma yai min kwarjini irinnaga maza suna kallona wlh.
Shakira tace to ai duk abinki baki kainiba wlh kokadan banasan yawan kallo saikiga mutum baki kalleshiba amma ya takuramiki da kallo saikace maye,
kinga ina zuwa barinazo mutafi dan ina tunanin yanzuma sun kusa tashi albashinsu kawai suke tsimayi.
Kamar kuwa kinsani inji zara tace.
Dan karfe biyar suke tashi kuma kinga yanzu saura minti ashirin kawai danhaka saiki sauri.
Ahankali shakira takimtsa bawata kwalliya tay sosaiba tunda dukansu sunsan inda zasuje danhaka basu damu dakayan dasuka sakaba 'yan matan suka feshe jikinsu da turare sai wani fitar dawani fitinannan kamshi suke sannan suka fito zuwa kawataccen falon inda suka iske umman shakira a zaune shikuma dadi tunima ya dade da fita.
A a ina kuma zakikaimin shakiran zahra u, umman shakiran ta tambaya,
wlh umma Abbane ya aikeni gurin 'yan aiki nakaimusu wannan kudin shine nakeso taimin rakiya,
tokingadai abbanku bayason yawan wannan yawonnaku danhaka duk yadda za ai kuyi kokari kudawo kafin magariba dan kar yadawo yatarar bakyanan ke shakira. Umman tata takara fada.
Shakira tace lah umma wlh yanzu zamu dawo ai babu nisa gurin.
Tace to adawo lpy Allah ya tsare.,
amin suka amsa sannan suka fita atare gwanin ban sha awa,
idan kagansu sai kace wasu taurari 2 wadanda suka fito sararin samaniya dan shan isaka da shakatawa.
Amotar zahra din suka tafi zaran ce take tukasu ahankali suna tafia suna hira gwanin ban sha awa babu yadda zakaga 'yan matan biyun dakuma nutsuwa da kwarjini da Allah yabasu basu burgekaba musamman ma shakira wadda ita duk kayan da tasaka saiyayi mata kyau sai kace wadda duk wata sutura dan ita akayi.
Asalin sunanta shamsiyya amma sabida yalwataccen gashi dan zankadaden hanci da Allah yai mata mahaifiyarta tasakamata shakira tun tana jaririya,
kamar wasa kuma tanafada mata cikin ikon Allah harkowa yadawo yake fada mata shikenan kuma shamsiyya tabata, harshikansa kuwa abbannata shakiran yake kiranta yanzu,.
Sunkusa isa gurin kenan sai kawai shakira taga zahra ta tsaya tayi fakin agefen titi.
Haba lpy zahra zaki tsaya anan bamu isobafa.
Eh nasani tafada sannan tamikoma shakira dubu darinnan tace dan Allah shakira kitaymaka kibasu idan mukaje dan wlh bazan iyay musu magana dan kwarjini zasuyimin.
Shakira tay murmushi tace yanxu kedan wannan shine kika tsaida mana da mota,
kinga zahra duk bala in tsoran namijin dakikefa saikinyi aure danhaka kisaki jikinki plss haba,
bani kudin,
tamikama shakiran sannan ta tada motar suka isa gurin.
Tunkafin sukarasa gurin suka hango yan aikin kowannensu yayi aiki yagaji musamman ma sale uwar raki tunkafin karfe 5 yadamu mutane da raki cewa shifa haryanzu baiga manajaba anya kuwa yau lpy.?
Babu wanda yakulashi dayagaji yadawo yazauna ajikn wata bishiya waishi adole yagama aikinsa naranar.
Akalla 'yan aikin sunfi su ashirin agun amma ahalin yanzu mutum 5 ne kawai suka rage asaman gidan suke aiki duk sauran sun sauko sunbi lapiyar inuwa cewarsu adole sungaji
Kowannensu yana zaune yana raki ganin yadda manajan haryanzu baizoba kwatsam saisukaga wata galleliyar mota tafaka
batareda jinkiriba wasu zukakan yan mata biyu suka fito daga cikin motar sannan cikin nutsuwa da taku mai tafiyar da hankali sukayo wajan 'yan aikin gaba dayansu sai suka karkata hankalinsu agun 'yan matan wasu dadama daga cikinsuma sun manta da labarin kudin aikin dasuke raki akai.
Abindaya kara basu mamaki shine yan matanfa wajensu suke yowa.
Musamman sale yafi kowa rikicewa dan harda tube wata hularsa kafiya naci iya tsammaninsa yam matannan gunsa sukazo
Sallamun alaikum, yan matan sukai sallama atare.
Wa alaikusalam gabadaya mazan gun suka amsa inka dauke nasaman ginin dasuke aikin rufin haryan wadanda su basuma san da zuwan 'yan matanba.
Shakirace taymagana.
Dan Allah kuyi hakuri nasan kunjima da jiran manaja amma baizoba yace asanar daku wlh ciwon cikinsane yatashi amma yaturomu mu wakilce shi.
Gabadaya mazan suka amsa da cewa Allah ya sawwake yakuma bashi lpy.
Sannan shakiran taci gaba dan Allah wanene shugaban naku tunda mu bamusan yadda kuke raba kudinba idanyaso saimu bashi yabaku.
Dukdacewa basu tsaida kowaba amma babu wanda kowa yafado zuciyarsa sai dan'tala.
Cikin hanzari sale ya mike tareda nuna dan tala asaman ginin yace gashi can hajiya.
Sannan ya kwala masa kira.
Dantala yajuyo sannan sale yace yaxo sunasan ganinsa.
Tun asaman shakira taymasa wani kallo nan take taji gabanta yabuga dakarfi abinda bata tabajiba acikin zuciyarta lokaci guda kuma saitaji tananeman tarasa nutsuwarta nan take....
NEXT PART 4&5