----FARKON LABARIN KENAN----
DANTALA!, DANTALA!! Tsohuwar takirawo sunan yaron nata har sau uku,
shikuwa yaja bargo sai bacci yakeyi,
haba dantala kaifa kace natasheku dawuri zaku tafi wurin aikin rufinnan dan kacemin idan mutum yamakara baza a barshi yafara aikinba amma kuma kadawo kakama bacci har bakwaima tawuce yakamatadai katashi karku makarafa.
Saurayin wanda ake tasa daga baccin yadan mitstsike idanunsa dakyar sannan yadanyi hamma tareda fadin alhamdulillah.
Ya dubi maman tasa yace subhanallah!
Wlh baba bansan rana tayi haka sosaiba shikuma wannan banzan yana gefena shima yana bacci amma koya kula.
Ya shuri kafar abokinnasa nakusa dashi tareda fadin kai sale katashi dallah lokaci yama kusa kurewa Allah yasa karma mu makara manaja yace bazamu samu aikiba yau.
Saurayin mai suna sale yadanyi mika tareda yin hamma baidamu dafadin alhamdilillah ba.
Yadubi dan tala daga gefe yace inbanda abinka dantala kaima baka tashiba ballantana kuma ni haba karka zama maison kai mana.
Dantala yai tsaki yace kaikenan kullum komai saidai ayimaka amma badai kayi dakankaba kokuma kayima wani dallah katashi lokacifa yana kurewa.
Sai anan tsohuwar tai magana tace kunga dai kuyi sauri nagama muku saura saikuyi sauri kuzo kuci karyai sanyi kutafi wajen aikin.
Dasauri kowannensu yatashi sukafara wanke fuskokinsu daruwa tareda wanke hannayensu wanda alokacin tsohuwar takawo musu sauran tuwon suka fara turashi baka.
.bayan sun cinye tuwanne sun samu 'yar nustuwa sannan dantala yadubi sale yace ina ka ajiye kayan aikin jiya damuka taso.
Salen yace suna wurin dana saba ajiyesu mana
dantala yace saikaje kadauko mutafi ai batareda bata lokaciba salen yashiga zauren gidan can bayan kyauren gidan sannan yadauko kayan aikin.
Bayan sun gama shiri dantala yashiga yai sallama da mahaifiyarsa tasakamasa albarka dayimasa addu ar dawowa lpy.
Yaji dadi sosai yay mata godiya suka fita shida abokinsa sale zuwa wajen aikin.
Bawani wajen zasujeba face wajen aikin rufin dasukeyi awani babban gida na wani alhaji.
Dantala yarone mai hankali tunda yataso bashida rashin ji gashi da sanin yakamata
mahaifiyarsa wato wacce yake kira da baba shikadai tahaifa sannan mahaifinsa yamutu tun baifi shekara uku da haihuwaba danhaka yataso maraya baisan mahaifinsaba sannan kuma baisan duminsaba.
Talakawane sosai wadanda suke bukatan taymako koda yaushe dan kullun sai dantala yafita aiki shida abokinsa sale suke samun saka wani abu acikin bakinsu na salati,
ranar da akasamu akasi kuwa ba asamu aikinba to tbbs gidannan dayunwa za akwana dan basuda cin kwana 2 ballantana kuma nasati.
Sana ar dantala da sale kenan kafinta.
Allah yabawa dantala fasaha da nasibi akan sana ar dan duk wani abu da aka bashi nagyara wanda yashafi bangare kafinta wato na buge buge kokuma joni to tbbs saiya hadamakashi.
Danhaka yake da farin jini agurin mutane sosai gashi kuma duk dacewa yakasance dan talaka.
Hakan baihanashi yatashi yanemi ilmiba na addini dana bokoba saidai nabokonne yaki cigaba lokacin daya kammala sakandire dakyar.
Sabida rashin kudi bisa dole ya hakura.
Allah yayishi da kyakykyawar sura gashida da farin jini agun mata da maza sauda dama 'yanmata suna nunamasa so.
Amma sabida yasan bashi da halin yin aure yanzu saiya nunamusu baima fuskanci abinda suke nufiba danhaka bisa dole suke janyewa koda kuwa wasu daga cikinsu sun gaji har suka furtmasa kalmar sone.
Babban abokinsa kenan sale wanda suke taredashi ayanzu saidai matsalar shi sale ba halinsu daya da dantalaba.
Yanada yawan karya sannan wasu lokutan akwai mugunta baidamu dayawan kula da addiniba dan wani lokacinma badan dantala yana takura masaba da bazai dinga yin wasu sallolinba dayake koda yaushe suna tare.
Sale bakine gajere mai matsakaicin kaurin jiki Allah yahada abotarsune lokacin da sale yaga fasaha da ilmi da Allah yabawa dantala wajen iya sarrafa katako ta kowanne hali dan haka yalike masa fiye da shekara biyar suna tare, asanadiyar abotarsune da dantala sale yacanza wasu halayya maras sa kyau da dama dayake taredasu.
Amma kuma duk dahaka ance mai hali baya fasa halinsa.
Samarin sun jere su 2 gwanin ban sha awa sannan suka nufi babbban gidan da ake aikin
aikuwa Allah yataimakesu dan har manajan yafara kirga yawan yan aikin da zasuyi aikin rufin yau sannan sukai sauri suma suka shiga layi aka kirga dasu.
Dayawansu kowa yasan dantala da hazakarsa dakuma iya aikinsa dan haka kowa yakeso ahadashi dashi,
musamman ma sabida fara arsa dakuma nuna rashin gajiyawa agurin aiki kodayaushe..
Afuwa Ku kasance tare da Ni akoda yaushe danjin cigaban wannan kasaitaccen labarin..