Shugaban Kasar Nigeria mai barin Gado Good Luck Ebele Jonathan Ya Nemi Yafiyar 'yan Nigeria da su yafe masa aduk inda yakai Kuskure.
Labari da ke zuwa ma Gidan Jaridar #AMINIYA Shugaba Jonathan ya Kara da Cewa"A Yafemin a duk inda nakai Kuskure a Lokacin da nake Mataimakin Shugaban Kasa, kawo Iyanzu da nake Shugaban kasa, wanda Wa'adin da aka dibarmin ya zo gangara."
Jonathan Ya kara da Cewa"Duk wani dan Adam Ajizine, wato mai yawan mantuwa."
Jonathan ya fadi Hakan ne Alokacin da aka shiryamai Ibadar Karshe ta bankwana a Babban Cocin da ke Gidan Gwamnati a Yau Lahadi.
Jonathan Ya kuma cewa"A Yi mai uziri ayafe masa duk abinda yakayi alokacin da yake Shugabanci domin abinda mutum yake tunanin idan yakai shine yafi da cewa ga Al'uma, amma sai Jama'a su kasa Fahimtar Sa."
A Karshe Shugaba mai barin Gado ya ce Jama'a su rika Hankalta Da Al'amura, da su yafe mai laifuffukan da Yaka Aikata abisa Rashin Sani, ko Kuma Acikin Kuskure da a Yafe masa."
Ko 'Yan Nigeria Zasu duba Kalaman Jonathan da Idon Basira da su yafe Masa Laifuffukansa...?
Title :
NA NEMAN GAFARAR 'YAN NIGERIA-JONATHAN
Description : Shugaban Kasar Nigeria mai barin Gado Good Luck Ebele Jonathan Ya Nemi Yafiyar 'yan Nigeria da su yafe masa aduk inda yakai Kuskure. La...
Rating :
5