A kalla mutane 800 ne suka rasa rayukansu a kasar Indiya sakamakon tsananin zafin da ake yi.Yanayin zafi a Indiya yana kai wa maki 48 ma'auin celcius a wasu yankunan.Galibin wadanda suka mutu mazauna jihohin Telangana da Andhra Pradesh ne inda mutane sama da 140 suka mutu tun ranar Asabar din da ta gabata. Yanayin zafi a Allahabad da ke Uttar Pradesh kuwa ya kai maki 48 ma'aunin celcius yayin da yanayin zafi a Delhi babban birnin kasar ya kai maki 44 ma'aunin celcius. Hukumomi sun bukaci mutane su zauna a gidajensu kum su rika shan ruwa da yawa.