Assalam Malam mune mukayi sallah muna idarwa sai liman yace ya manta yayi fitsari baiyi tsarki ba.
Shin zamu maida wata sallah ne kokuwa ta limance kadai ta6aci, tunda mu da tsarkinmu ko har tasama tayi daidai ???
AMSA:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To dan uwa sallar liman ta6aci, kuma dole ya sake.
Amma ku sallarku ta inganta, a zancen mafi yawan malamai.
Saboda dalilai kamar haka:
1. An rawaito daga Umar- Allah ya yarda da shi cewa:
Yataba yiwa mutane limancin sallar asuba, bayan angama sallah, sai yaga maniyyin mafarki a jikin tufansa, sai yasake sallah, amma mamun basu sake ba.
2. Sayyidina Aliyu yana cewa:
"Idan mai janaba yayiwa mutane limanci, zan umarce shi yayi wanka, yasake sallah, amma bazan ce da mamun su sake sallah ba.
3. Abdullahi dan Umar - Allah ya yarda dashi - yata6a yiwa mutane sallar asuba, sai yatuna bashida alwala, sai yasake amma mamu basu sake ba.
Abin daya gabata aikin sahabbai ne, aikin sahabi hujja ne, in ba'a samu wani sahabin yasaba masa ba.
Domin neman Qarin bayani duba: Almugni 1\419.
Allah shine mafi sani.