* Kullum idan ka farka daga barci, ka bude bakinka da zikirin Allah.
* Ka je ka tsarkake jikinka sannan ka tafi Masallaci kabi jam'i (kar ka bar jam'i ya wuce ka). Idan baka samu jam'i ba, Kayi ta a Masallacin yafi alkhairi fiye da yinta adakinka.
* Kar ka manta da Raka'atayil Fajri. (raka'o'i biyu kafin sallar asuba) domin sun fi duniya da abin cikinta alkhairi awajen Allah.
* Bayan ka idar da sallah kayi ma kanka addu'a da iyayenka, da danginka, da dukkan musulmai baki daya.
* Ka zauna awajen ka karanta Azkar dinka (zikirorin da ake yi safiya da maraice domin godiya ga Allah, da kuma neman tsarinsa daga dukkan sharrukan.
* Ka dauko Alqur'aninka ka bude ka karanta abinda ya sawwaka. Koda Hizifi guda ne.
* Ka Qara wanke zuciyarka daTasbeehi, Istighfari, da Hailala...
* Sannan ka Qamsasa ruhinka da Salati da tasleemi bisa Shugaban Halittun Allah baki daya, Annabinmu MUHAMMADU (saww).
* Idan ka idda, kayi addu'a, kai da kanka zaka ji wani irin haske acikin zuciyarka. Haka zaka wuni acikin wannan hasken In sha Allahu.