BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
Tsira da aminci su tabbata bisa zababben Annabin da babu kamarsa, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da sahabbansa madaukaka.
Acikin wannan darasin zamu dan kawo muku Takaitaccen tarihin matayen Manzon Allah ne (saww).
Kasancewarsu iyayen kowanne mumini, Kuma kasancewarsu sune kadai Matayen da Allah ya zabosu daga cikin dukkan bayinsa domin su zama Mataye ga Fiyayyen Masoyinsa (saww). Kuma kasancewarsu sune manyan Malaman da suka karbo mana ilimai irin na zamantakewar aure da sauran hukunce hukuncen abubuwan da sukan faru acikin gida...
Idan muka dubi wadannan dalilan, to tabbas zamu fahimci Muhimmancin Sanin tarihin wadannan tsarkakan bayin Allah wadanda babu shakka Allah ya fifitasu sama da dukkan matayen wannan al'ummar.
KHADEEJAH BINT KHUWAILID (RA)
***********************************
NASABARTA: ita ce Khadeejatu 'yar Khuwailid, 'dan Asad, 'dan Abdul Uzza. Shi wannan Abdul Uzza din, Shaqiqin Abdu Manafi ne, wato Mahaifansu guda dashi da Kakan Manzon Allah (saww).
Sunan Mahaifiyarta Fatimatu bnt Za'idah bn Al-Aiham.
Sayyidah Khadeejah tana da 'yan uwa guda uku. sune Haalah (namiji ne) sai kuma Khaalidah da Ruqayyah.
SIFFOFINTA: Ita mace ce madaukakiya daga cikin matayen Quraishawa. Kuma mace ce mai gaskiya da rikon amana, kuma mai mutukar tausayi
Ita 'yar asalin dangi ce. Kuma tana da kyawun halitta da kuma dukiya. mutanenta suna girmamata sosai.
Ita ce farkon matar da ANNABI (saww) ya aura. Kuma ya zauna tare da ita tsawon shekaru 25 bai mata kishiya ba.
Ita ce farkon shiga musulunci. Kuma ta sallama dukkan kanta da abinda ta mallaka zuwa ga Manzon Allah (saww).
Bukhary da Muslim duk sun ruwaito cewa Ubangiji ya aiko ma Nana Khadeejah da gaisuwa ta musamman kuma yayi mata albishir da wani gida acikin Aljannah wanda aka Qerashi daga Farin Lu'ulu'u, kuma babu hayaniya ballantana Wahala acikinsa.
Annabi (saww) ya kasance yana cewa: "MAFI ALKHAIRIN MATAYEN (WANNAN AL'UMMAR, ITA CE KHADEEJATU BINTU KHUWAILID. KUMA MAFI ALKHAIRIN MATAYENTA (WATO MATAYEN BANU ISRA'IL) ITA CE MARYAM BINTU IMRAAN".
A wani hadisin kuma yace "DA YAWA DAGA CIKIN MAZAJE SUN SAMU CIKA (WATO CIKAR IMANI) AMMA BABU WADANDA SUKA SAMU CIKA DAGA CIKIN MATAYE IN BANDA GUDA HUDU:
1. AASIYA BNT MUZAAHIM (MATAR FIR'AUNA).
2. MARYAM BINT IMRAAN (MAHAIFIYAR ANNABI EISA).
3. KHADEEJAH BINT KHUWAILID.
4. FATIMATU 'YAR MUHAMMAD (SAWW).
(Bukhary da Muslim).
Sayyidah Khadeejah ta kasance tamkar Waziriya ga Manzon Allah (saww) wajen isar da sakon musulunci. Tarihi ya nuna cewa ta kasance tana yin sallah tare dashi da Sayyidi Aliyu bn Abi Talib ajikin Ka'aba tun sannan ba'a wajabta sallar ba.
Kamar yadda na gaya muku, Manzon Allah (saww) ya aureta alhali shi yana da shekaru 25 aduniya. Ita kuma tana da shekaru 40. Amma Allah cikin ikonsa ya tarfa mata albarka sosai domin ita ce mahaifiyar 'ya'yan Manzon Allah (saww) har guda 6.
Sune Alqasim, Abdullahi (At-Tahir, At-Tayyib) da Zainab da Ruqayyah da Ummu Kulthum da Fatimah (Amincin Allah ya tabbata ga mahaifinsu dasu baki daya). Ibraheem Almu'azzam shine kadai wanda ba ita ce ta haifeshi ba.
Manzon Allah (saww) ya aureta ne tana bazawara. Amma Mijinta na farko ana kiransa Hind bn Nabbash bn Zuraarah At-Tameemy.
Ya mutu tun zamanin Jahiliyyah kuma ta haifa masa 'ya'ya maza guda biyu. Sune Hindu da Haalah. Dukkansu sun riski Musulunci harma sun Musulunta. Kuma suna daga cikin Sahabban Annabi (saww).
Bayan Rasuwarsa ta auri 'Ateeq bn 'Aabid ko 'Aa'iz Almakhzumiy. Shi kuma ta haifa masa 'ya mace, sunanta Hindu. Ta musulunta har ma tana daga cikin matayen Sahabban Annabi (saww).
Lokacin da Annabi (saww) ya aureta yayi mata Sadaki da RAKUMA 20 (Wannan sadakin ya haura Naira Million guda a kudin yanzu).
Nana Khadeejah ta rasu ne agarin Makkah, acikin watan Ramadhan, Shekara ta uku kafin Hijira. Kuma anan aka binneta.
Annabi (saww) yana kiran shekarar rasuwarta da suna SHEKARAR BAQIN CIKI.
Nana Khadeejah ta ruwaito hadisi guda daya ne rak daga Manzon Allah (saww).
Na san wasu zasuyi mamakin Qarancin hadisin. Amma ba abin mamaki bane. Domin ita alokacin zamanta da ANNABI (saww) ba'a fara rubuta hadisai ba. Ba don haka ba, da sai ta zarce kowa ruwayar hadisi. Idan anyi la'akari da dadewarta tare dashi (saww).
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP :