Manchester United ta amince da yarjejeniyar dauko dan kwallon PSV Eindhoven Memphis Depay a karshen kakar wasan bana.
Kudin da United din za ta dauko dan kwallon zai kai fam miliyan 25 zuwa 30, a inda zai taka leda har zuwa kashen kakar 2019 da kuma zabin zai iya kara shekara daya.
Likitoci za su duba lafiyar dan wasan mai shekaru 21 a mako mai zuwa, zai kuma koma United ne da zarar an bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa a Junin badi.
Depay wanda ya buga tamaula karkashin Louis van Gaal da tawagar kwallon kafar Holland, yana daga cikin 'yan wasan da PSG da Liverpool suka yi zawarci.
source bbchausa.com
Title :
Man United ta amince ta dauko Depay
Description : Manchester United ta amince da yarjejeniyar dauko dan kwallon PSV Eindhoven Memphis Depay a karshen kakar wasan bana. Kudin da United din z...
Rating :
5