Assalamu alaikum warahmatullah.
na kasance mai sha'awa sosai, ina yawan fitar
da maziyyi amma bani da
halin yin aure. Kuma azumi in na dauka da kyar
nake kaiwa sai zazzabi da ciwon
ciki ya kamani.
Na kammala jami'a amma ban samu aikin yi ba,
balle in yi aure.Tun ina jami'a
macce ko cikin aji ne, in dai ta yi min magana
maziyi na iya fitowa ko da kan
harkar karatunmu ne.
Kuma ina fama da 'extreme shyness/social
phobia' ko meye maganinsa?.
AMSA
=====
WA ALAIKUMUS SALAM WA RAHMATULLAH.
1. Babban Maganin matsananciyar sha'awa,
Shine KAYI KOKARI KA SANYA
TSORON ALLAH AZUCIYARKA.
Koda kana da auren idan zuciyarka ta zamto
babu tsoron Allah, wannan ba zai
hanaka kalle kallen haramtattun abubuwan da
zasu motsa maka sha'awarka ba.
Sannan shi aure shine mataki na biyu. Kuma
kace baka da ikon yinsa saboda
rashin sana'a. Kuma kace wai baka iya kaiwa
azumin nafila idan ka dauka. Sai da
kyar kake iyawa.
Shawarar da zan baka anan ita ce: Kar ka
dogara da karatun boko kadai
arayuwarka. Zai fi kyau amatsayinka na matashi,
kaje ka nemi wata sana'ar
hannu wacce zaka rika samun kudaden
kashewa, da kuma biyan bukatunka.
Misali kamar Aikin Cafenter, bakanike, Ko kuma
kasuwanci. kowanne daga cikin
ukun nan zai iya rikeka insha Allahu harma ka
samu abinda zakayi auren,har ma
ka taimakawa mahaifanka da 'Yan uwanka. in
Allah yaso.
Kafin nqn, Wajibi ne ka sanya tsoron Allah
azuciyarka. Sannan ka rika yawaita
karatun Alqur'ani, da zikirin Allah ako yaushe.
Kuma ka nisanci kalle kallen
haramun, ko shiga shafukan batsa, da dai
sauransu.
Shan leman tsami acikin Shayi, tare da shan Jar
kanwa yakan rage ma mutum
yawan sha'awa. Insha Allahu.
2. Shawararka wacce ka bayar cewa mu
tsawatar da 'Yan uwa mata akan sanya
hotunansu da sukeyi akan shafukan Facebook,
Twitter, da dai sauran kafofin
internet. Wannan shawarar tana da kyau.
Yana da kyau 'Yan uwa mata kuji tsoron Allah
ku dena bayyana abinda Allah ya
wajabta muku boyewa. Duk matar da take
tunanin gamuwarta da Allah ba zata
rika watsar da kanta a interbet ba. Kuji tsoron
Allah ku tuna da lahirsrku ku dena
fitinar da kanku da kuma wasu mazajen.
3. Yanayin matsananciyar kunya wacce kace
kana da ita, ai wannan abin yabo ne.
bai kamata har ka rika damuwq ba.
Manzon Allah (saww) ya gaya mana
muhimmancin kunya, da fa'idodinta acikin
ingantattun hadisai da dama.
Akwai hadisin da yace "KUNYA TANA DAGA CIKIN
IMANI, DUK WANDA BASHI DA
KUNYA, TO BABU IMANI GARESHI. "
Awani hadisin kuma yace : "KUNYA ALKHAIRI CE
GABA DAYANTA".
Don haka ka gode ma Allah da ya baka kunya.
4. Ka manta baka fadi Qualification dinka, da
kuma fannin da ka karanta ba.
Watakil akan shafin nan ka samu wasu bayin
Allah wadanda zasu taimaka maka
su samar maka da aikin.
Amma dai fatanmu gareka shine: Allah ya datar
dakai ka samu aiki na halal, ya
Qara rufa ma asirinka, ya tsare maka imaninka
da kumq dukkan jikinka daga
ayyukan sa'bo.
WALLAHU A'ALAM