TAMBAYA TA 1611
*******×***********
Assalamu Alaikumm Allah yataimaki malam Allah yaqara daukaka darajarka Allah yasaka maka da Alkhiari Akan fadakarwar da kake dan Allah.malam Ataimaka a amsa min wannan tmbyr itace ta 3 kenan a wadanda na.aiko baa Amsa min ba
1..Shin ya hallata mutum ya nemi maganin kasuwa idan yana kasuwanci?
2..Malam idan hakan bai hallata ba wacce Addua mutum zai dinga yi dmn neman budi Agun Allah
3..Sannan malam taya mutum zai dinga godewa Allah idan wata niima ta sameshi?
dan Allah malam Ataimaka a amsa min wannan tambyr dmn ragowar Alumma su Amfana.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Hakika addinin nan namu na Musulunci bai kyalemu haka ba. Sai da ya tanadar mana da abinda zamuyi aduk cikin halin da muka shiga.
Irin wannan laluben neman maganin kasuwa, maganin Farin Jini, maganin bindiga, da sauransu, shi yake jan mutum zuwa ga kauce ma hanyar Allah da Manzonsa (saww).
Zai fi kyau amatsayinka na Musulmi ka dogara ga abinda aka karbo daga Manzon rahama (saww) Wato ina nufin Azkar da addu'o'i ingantattu.
Misali kamar wannan: "LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LAA SHARIKA LAHU. LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU. YUHYEE WA YUMEETU, LA YAMUTU ABADAN BIYADIHIL KHAIRU WA HUWA ALA KULLI SHAY'IN QADEER".
Manzon Allah (saww) yace duk wanda ya fadi wannan zikirin ayayin shigarsa kasuwa, Allah zanyi rubuta masa lada Miliyon guda. kuma zai kankare masa zunubansa. (Ka duba Al-azkar na Imam Nawawy).
Sannan akwai irin su "BISMILLAHIL LADHEE LA YADHURRU MA'A ISMIHEE SHAI'UN FIL ARDH WALA FIS SAMA'I WA HUWAS SAMEE'UL ALEEM.
Wannan Addu'ar Manzon Allah (saww) yace duk wanda ya karanta sau uku da safe, to a wannan yinin babu wani abinda zai iya chutar dashi. To ashe kenan idan 'Dan kasuwa ma ya riketa yana yi ko yaushe to In sha Allahu Ubangiji zai sanya alkhairi da albarka acikin kasuwancinsa. ba zai ga yawaitar asara ba.
'Dan uwa gara ka rike wadannan addu'o'in ka kyale duk wadancan abubuwa.