TAMBAYA TA 1606
*********************
Assalamu alaikum, Malam barka da aiki ya hidima da mutane Allah ya saka muku da mafificin alkairi.
Tambaya ta Malam akan wani ganye ne da hausawan mu ke masa laqabi da qaiqayi koma kan masheqiya. shin wannan ganye yana maganin sihiri ne? In yana yi ya ake sarrafa shi?
Jazakallahu khairan.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah.
Eh gaskiya ne hausawa sukan yi amfani dashi wajen karya sihiri. Suna rubuta ayoyin karya sihiri ne sannan su sanya shi garin wannan ganyen acikin ruwan, sannan su rika shansa suna shafawa ajikinsu.
Amma fiyayyen makarin Sihiri shine Ganyen Magarya, Garin hilteet, Man Zaitun da Man habbatus sauda.
Ki samu ganyen magarya guda bakwai, (ko kuma 41 in ji wasu maluman) ki dandaka akan dutse, sannan ki samu ruwa acikin Bokiti ko Kwarya, ko kwano.
Ki zuba wannan dakakken ganyen magaryar acikinsa, sannan ki sanya babban yatsanki acikin ruwan. Ki karanta ayoyin karya sihiri aciki. Kuma kina kusantar da tiririn karatun zuwa kan ruwan.
Idan kin kammala sai ki rika shan ruwan kuma kina wanka dashi awaje mai tsarki.
Shi kuma Hilteet ki rika yin hayaki dashi ku. a kina sanyawa acikin abincinki. Man Zaitun da man habbah ki karanta ayoyin karya sihiri da ayatush shifa'i acikinsa sannan ki rika shansa kina sanyawa acikin abincinki kuma kina shafawa ajikinki.
In sha Allah sihirin zai karye kuma zaki samu lafiya da izinin Allah. kuma bayan wannan akwai wasu hanyoyin karya sihirin zamu fadesu anan ZAUREN FIQHU nan gaba in sha Allah.
WALLAHU A'ALAM.