TAMBAYA TA 1588
*******************
Ina fatan malam ya tashi lafiya? Ina Kuma yi wa malam fatan alkairi. Allah ya kara ilimi. Ya kuma gafarta wa mahaifa. Ameen.
Malam matatace take matukar son abubuwan da za su gyara mata nononta (kamar wadda za su taimaka wajen tsayarwa da kuma girma). Domin ta matsamini da in samar mata da kayan cosmetics irinsu breast firm cream, breast enlargement cream. Amma ni banason tayi amfani da wannan cosmetics din saboda abinda za su iya haifarwa gaba.
Malam saboda hakan nake mika bukatata a gareka domin a taimaka mana. Daga mai bin shafin Zauren fiqhu yau da kullum.
Nagode.
A. Abdul...
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Acikin dukkan dukkan tsirrai da abubuwan da suke gyara ma Mace Qirjinta, babu kamar HULBA.
Ka gaya ma matar taka ta samu Cokali guda na hulba ta rika dafawa kullum da safe tana sha da zuma, Sannan da yamma ma haka.
Taci gaba da yin haka har tsawon kwana 30 ko 40. In sha Allahu zata ga abun mamaki.
Sannan SI'ITIR Shi ma yana gyara Qirjin Mace sosai. Idan ana dafawa ana sha.
Mqn hulba da Man SI'ITIR duk suna da amfani sosai. ana sha, kuma ana shafa ma Qirjin. in sha Allahu za'a dace.
WALLAHU A'ALAM.