TAMBAYA TA 1594
******************
ASSALAMU ALAIKUUM WARAHMATULLA. Malam Allah yasaka da alkhairi abisa.dawainiya da kake damu. Malam Dan Allah Malam Inaso a fadamun maganin FITSARIN KWANCE domin walahy tun INA karami nake fama da wannan lalura.
Kuma yanzu Malam Inada shekaru ashirin. Kuma Malam anyi maganin amma har yanzu Allah bai sa mun dace ba. Shine nakeso Malam Dan Allah ataimaka min koda wani Abu. Nagode Malam Allah ya biyaka da gidan Aljanna. Ameeen
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Hakika matasa da yawa suna fama da irin wannan matsalar. Amma hanyoyin magancewa suna da sauki sosai. sai dai kuma suna bukatar nacewa yau da kullum arika yi ba tare da denawa ba.
Abubuwan da zakayi sun hada da:
1. Lazimtar Karatun Alqur'ani da zikirin Allah safe da yamma.
2. Ka kasance tare da tsarki da alwala ayawancin lokutanka. Har ma lokacin barci.
3. Ka lazimci yin Ta'aweezi yayin shiga bandaki, kuma karika karanta Ayatul kursiyyi da falaki da Naasi ayayin da zaka kwanta barci.
4. Ka kula sosai da sallolinka na farillah, kuma ka lazimci nafilfilin dare da rana.
5. Ka samu bawon Qwan kazar gida, ka wankeshi sosai. Sannan ka nikashi ya zama gari. ka rika hadawa tare da garin Habbatus Sauda da garin Alkama ka zubasu acikin zuma kana shan cokali 2 safe da yamma.
In sha Allahu idan kabi wadannan matakan zaka samu waraka da izinin Allah.
WALLAHU A'ALAM.