Assalamu alaykum Allah ya karawa malan lafiya ilmi da takawa amin.Dan Allah mln a karanta wannan tambaya tawa. malan Dan Allah maganin farfadiya da yawan yawan gudawa na ke so a taimakamin da shi.ko da ta wannan adireshin ne.wallahi Malian wani makusanci na nee ya ke fama da wannan matsalar.Allah ya taimaki Malian.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Dangane da farfadiya, Ka samu Garin Dattora kamar cokali 3, ka hada da garin Hiltit shima haka. Sai arika turara masa ana yi masa hayaki dashi. In sha Allahu za'a dace.
Sannan asamu garin Fijil cokali 3, garin Habbatus Sauda shima haka. Sannan a gaurayasu tare da Garin Kustul Hindi da kuma dattora cokali 2.
Ajuyesu acikin zuma, arika bama marar lafiyan cokali biyu da safe kafin yaci komai. sannan da yamma bayan magriba asake bashi. In sha Allahu zai yi masa maganin gudawar da kuma farfadiyar da izinin Allah.
WALLAHU A'ALAM.