Mai tsaron bayan Real Madrid Dani Carvahal ya ce sun yi ban kwana da kofin La Ligar bana, bayan da Barcelona ta ba su tazarar maki hudu tsakani a ranar Asabar.
Madrid ta tashi wasa 2-2 da Valencia a gidanta, bayan da Barcelona ta ci Real Sociedad 2-0 a karawar da suka yi wasan mako na 36.
Barcelona na bukatar doke Atletico Madrid ko kuma Deportivo La Coruna kafin ta dauki kofin bana karo na 23, yayin da Madrid ta dauka sau 32.
Carvahal ya ce bai kamata su zubar da damarsu ba a gida, saboda haka sun yi ban kwana da kofin bana.
Za a tsayar da wasannin kasar Spaniya sakamakon takaddama tsakanin hukumar kwallon kafar kasar da gwamnati bisa rabon kudaden nuna wasannin kasar a talabijin.
Title :
Madrid ta hakura da La Ligar bana —Carvajal
Description : Mai tsaron bayan Real Madrid Dani Carvahal ya ce sun yi ban kwana da kofin La Ligar bana, bayan da Barcelona ta ba su tazarar maki hudu tsak...
Rating :
5