Sabon gwamnan Jahar Filato, Barrister Simon Lalong ya yi sha alwashin ganin cewa Jahar Filato ta koma kamar yadda aka santa a da.
Sabon gwamnan Jahar Filato, Barrister Simon Lalong ya yi alkawrin zai hadaka kan ‘yan jahar a shekarun da zai yi yana mulkin.
Lalong ya bayyana hakan ne a lokaicn da aka rantsar da shi a yau juma’a inda ya kara da cewa zai magance sauran matsalolin jahar da suka hada da yajin aikin ma’aikata.
Baya ga haka sabon gwamnan ya ce gwamnatinsa na bukatar hadin kan dukkanin jama’ar jahar domin a magance wadannan matsaloli ciki har da na satan shanu.
Har ila yau Lalong ya yi alkawarin inganta rayuwar al’umar Jahar ta hanyar inganta tattalin arzikin jama’a da suka hada da noma, zaman tattaunawa da al’umomin da ba sa ga maciji da juna.
Gwamnan ya kuma ce zai sake gina sabuwar kasuwar Jos, wacce aka fi sani da Terminus Market.
A can Jahar Nasarawa da ke makwabtaka da Filaton, gwamna Tanko Al Makura, ya yi alkawrin kara inganta rayuwar al’umar Jahar a wannan wa’adin mulki na biyu.
Ga karin bayani a rahoton Zainab Babaji: