Wata Sahabiyyah Baqar Fata ('Yar Asalin Africa) tazo ta samu Manzon Allah (saww) yana zaune sai tace masa "Ya Rasulallahi ni ina faduwa (Wato Aljanu suna jefar dani) Kuma ina yin tsaraici.. Ina so ka roka min Allah".
Sai yace "IDAN KIN SO, KIYI HAKURI ZAKI SAMU ALJANNAH. IDAN KUMA KIN SO, ZAN ROKI ALLAH YA WARKAR DAKE".
Sai tace "Zanyi Hakurin, amma ina so ka roka Min Allah, in dena yin tsaraicin".
Sai Annabi (saww) ya roka mata Allah. Tun daga ranar koda Aljanuysun jefar da ita batta yin tsaraici.
'Yan uwa ku dubi hakuri da kuma juriya bisa samun babban rabo irin na wannan Matar. Ta zabi tayi hakurin zama da jinyar, idan ta mutum kuma ta samu shiga Aljannah.
Tun daga wannan ranar, Sahabbai suke ce mata 'Yar Aljannah...
Anan nake jan hankalin 'yan uwa masu fama da irin wannan larurar cewa Su dangana ga Allah. ku sani cewa Allah shi kadai ne mai warkarwa. Waninsa ba ya warkarwa.
Kuma ku sani cewa neman magani ba laifi bane. abu ne halastacce. Hasali ma, Annabi (saww) da kansa ya bada umurnin cewa anemi magani. Amma fa anemeshi ta hanyar da Allah ya halatta.
Amma wajibi ne mu sanya dogaro ga Allah azukatanmu. Mu dena gaggawa, mu dena sanya kokwanto cikin magungunan Musulunci, ko kuma addu'o'in da muke yi.