Abu Abdillah Al Khurasaniy (rah) ya bamu labari yana cewa :
"Akwai wani Sarki daga cikin sarakunan Qasar Khurasaan (wato Afghanistan) yana da Wani Khadimi wanda yake yi masa hidima.
Yayin da shi wannan Khadimin ya daura niyyar tafiya zuwa Hajji, sai ya nemi izinin Shugabansa. Wato wannan sarkin kenan.
Sai sarkin ya ki yin izini gareshi. Sai yace masa "Na nemi izininka ne fa akan abinda ya shafi bin Allah da Manzonsa".
Sai shi kuma sarkin yace : "Ba zan yi maka izini ba har sai ka dauki alkawarin zaka biya min tawa bukatar. Idan ba zakayi haka ba, to ni kuwa ba zanyi kama izinin ba".
Sai Sarkin yace "Zan hada ka da abin hawa, da guzuri, da kuma bayi (wadanda zasuyi maka hidima) amma idan ka isa Qabarin MUSTAPHA MUHAMMADU (SAWW) kace masa: "Ya Rasulallahi, Ubangidana yace in gaya maka BABU RUWANSA DA ABOKAN KWANCIYAR NAN NAKA GUDA BIYU (Wato Abubakar da Umar r.a).
Sai wannan Khadimin yace "Nace masa to naji kuma zan bi.. (amma ba haka nake nufi acikin zuciyata ba).
Yayin da na isa Birnin Madeenah, naje na tsaya agaban Qabarin nayi sallama ga Manzon Allah (saww) na juya nayi ma Abubakar da Umar. Sai kunya ta hana in isar da wannan Mummunan sako wanda aka aikoni dashi.
Ina cikin haka sai barci ya daukeni.. Acikin masallacin. Kawai sai naga Bangon Qabarin ya tsage, sai naga Manzon Allah (saww) ya fito yana sanye da korayen tufafi masu haske. Ga kuma Qamshin Almiski (irin wancan na Aljannah) yaba tashi ajikinsa.
Sai ga Abubakar agefen damansa, Umar kuma agefen hagun dinsa. Su ma duk suna sanye da Korayen tufafi masu haske.
Sai Manzon Allah (saww) yace min "YA KAI WANNAN MUTUM, MENENE YA HANA BAKA ISAR DA SAKON DA AKA AIKOKA DASHI BA??".
Sai na mike tsaye don girmamawa saboda kwarjinin Manzon Allah (saww) sai nace masa: "Ya Rasulallahi, ni ina jin Kunyar in jiyar da kai wata mummunar magana akan wadannan Sahabban nan naka guda biyu".
Sai yace min "INA SANAR DA KAI CEWAR ZAKAYI AIKIN HAJJINKA LAFIYA KALAU KUMA ZAKA KOMA KHURASAN CIKIN KOSHIN LAFIYA IN SHA ALLAHU.
AMMA IDAN KAJE WAJEN UBANGIDAN NAKA KACE MASA: MANZON ALLAH (SAWW) YACE IN GAYA MAKA :
"HAKIKA ALLAH DA KUMA NI, BABU RUWANMU DA DUK WANDA YAKE BARA'A DAGA GARESU... SHIN KA FAHIMTA?"
Sai nace "Eh na fahimta". Sai yace mun "KUMA KA SANI CEWA KUMA SHI ZAI MUTU BAYAN KA ISA WAJENSA DA KWANA HUDU. SHIN KA FAHIMTA? "
"KUMA KA SANI CEWAR WANI QATON MARURU ZAI FITO MASA AKAN FUSKARSA KAFIN YA MUTU".
Daga nan sai na farka. Nayi godiya ga Allah abisa ganin Annabi (saww) da nayi aciki barci, tare da Abokan kwanciyar nan nasa guda biyu.
Kuma na gode ma Allah abisa kiyayeni da yayi daga isar da wannan mummunan Sako.
Daga nan sai nayi aikin Hajji har na dawo gida cikin koshin lafiya. Na taho ma Ubangidan nan nawa da tsaraba da kayyaki.
Kwana biyu bai ce min komai ba, sai a rana ta uku yace min "Yaya Kayi da bukatata?
Sai nace masa "eh Bukatar ta biya".
Sai yace "To gaya min yadda akayi".
Sai nace masa "Ya kai Ubangidana, ba zaka so kaji yadda abin nan yake ba. "
Sai yace "ai dole sai ka gaya mun".
Sai na gaya masa dukkan labarin abinda ya faru. Da na gaya masa abinda Annabi (saww) yace in gaya masa, sai yayi dariya. Ya fadi wasu kalmomi irin na Kafirci.
Washegari, rana ta hudu kenan sai ga wani Qaton maruru ta fito masa a fuska. Kafin sallar azahar ya mutu har mun binneshi.
Ya Allah ka shiryi masu Qin Abubakar da Umar (ra) idan kuma ba zasu shiryu ba, Ya Allah kayi fito na fito dasu irin wacce kakeyi da masu chutar da waliyyanka.