Abbaad Alkhawwas ya bamu labari cewa:
"Watarana Annabi Musa (as) ya fita daji domin biyan wata bukatarsa sai ya tarar da wani Mutum atsaye acikin dajin, yana ta addu'a, ya cira hannayensa sama yana rokon Allah yana kuka!!
Sai Annabi Musa (as) ya tsaya yana ta kallon wannan mutumin har tsawon wani lokaci. Sannan yace ma Ubangiji :
"YA RABBI, KA AMSHI ADDU'AR BAWAN NAN NAKA MANA! ".
Sai Allah yayi masa wahayi cewa: "YA MUSA, DA ACE WANNAN MUTUMIN ZAI YI TA TSALA KUKA HAR RANSA YA FITA, KUMA YACI GABA DA 'DAGA HANNAYENSA YANA ROKONA HAR HANNUN NASA YA TA'BO SARSRIN SAMANIYA, BA ZAN AMSHI ROKONSA BA!".
Sai Annabi Musa (as) yace "SABODA ME?".
Sai Ubangiji yace masa: "SABODA YANA CIN HARAM, KUMA TUFAFIN JIKINSA MA NA HARAM NE, KUMA YANZU HAKA MA AKWAI HARAM DIN ACIKIN GIDANSA".
Sai Annabi Musa (as) ya tafi gidan wannan mutumin yayi bincike sosai. Sai ya samu Dirhami goma sha shida (16) na haram acikin gidan..
– Ibnul Jawziy ne ya kawo wannan Qissar acikin littafin 'UYOONUL HIKAAYAT shafi na 353 - 354.
TSOKACI
*********
In dai har Allah - Duk da tausayinsa da rahamarsa - zai ki amsar Addu'ar mutumin nan saboda CIN HARAM DA YIN SUTURA DA HARAM, DA KUMA AJIYAR KUDIN HARAM, to yaya kake zaton halin da mutanenmu na yanzu suke ciki??
A yanzu zaka ga mutum ya debi dukiyar al'ummah ya gina Manya manyan gidaje a manyan biranen Qasar nan, Ya sayi Manyan motoci, ya ajiye MILIYOYIN DALOLI acikin asusun bankuna... KUMA DUK JAMA'A SUN SAN CEWA BA KUDIN HALAL BANE.. Shi ma kansa ya sani..
Amma babu mai kyamarsa, Babu Mai zuwa ya Wa'azantar dashi, ballantana yaji tsoron Allah. Maimakon haka ma sai dai kaga Malamai suna binsa har gida suna yi masa fadanci. Suna yabonsa acikin Wa'azinsu, wai saboda 'yar gudunmuwar kudinsa wanda Allah ma ba zai karba ba!!!
Iyayen Zamanin nan sun gwammaci su bama MACIYIN HARAM auren 'yarsu, maimakon su bama Maciyin halal, wanda albashinsa kadai ya dogara dashi. ko kuma wani mai sana'ar hannu!!
DAGA ZAUREN FIQHU :