HALIFAN MUSULUNCI, Almutawakkil yana da wata kuyanga wacce yake sonta sosai. Rannan sai wani Aljani ya bugeta, ta fadi Qasa, tana ta eehu.
Sai Halifan ya aika wa Imam Ahmad bn Hanbal cewa yazo yayi addu'a akan abun.
Sai Imam Ahmad ya bayar da takalmansa wadanda yake sawa in zai yi alwala. Yace akai ma aljanin Wadannan takalman, a tambayeshi SHIN ZAI FITA DAGA JIKIN WANNAN KUYANGAR, KO KUMA A DAKESHI DA WADANNAN TAKALMAN SAU SABA'IN? "
Sai Aljanin yace : "NAJI KUMA NA BI!! Da ace Imamu Ahmad zai ce dukkanmu (Aljanu) kar mu zauna acikin yankin Iraqi, Wallahi da ba zamu zauna ba!! Imamu Ahmadu ya bi Allah, kuma duk wanda ya bi Allah dole komai ya bishi!!".
Yana fadin haka sai ya fita daga jikin Matar... Ta samu lafiya sosai harma ta haifi 'Ya'ya da dama.
DAGA ZAUREN FIQHU.