1. Ka zamto mai hakuri da kawar da kai.
2. Ka kasance mai Juriya da dauriya akanta.
3. Ka zamto mai yawan bata shawarwari da gyara mata inda tayi ba daidai ba.
4. In ranta ya baci ka kwantar da hankalinta.
5. In tayi girki ko kwalliya ka yaba.
6. In ta maka karamin laifi ka hadiye, in kuma babba ne ka mata nasiha.
7. Ka zama mai yawan fara'a da murmushi gareta, kar ka zama mai daure fuska kamar bijimin sa.
8. Ka cigaba da tattalinta domin haka ka nuna mata lokacin tana gidansu.
9. Kar ka kashe mata gwiwa yayin da ta maka shagwaba ta hanyar cewa ke har yanzu ba kya girma, ko menene kike wani abu haka kamar yarinya?
10. Kar ka daka mata tsawa, nasiha tafi.
11. Kar ka aibata ta da mummunar magana, wawiya, shashasha, banza, sakarai, sokuwa, bagidajiya da sauransu.
12. Ka cika mata hakkinta na auratayya a matsayinka na da namiji ya kasance ta gamsu da kai.
13. Nuna mata yan uwanta naka ne kamar yanda naka suka zama nata.
15. Yabonka akan ayyukanta da suka birgeka zai karfafa mata gwiwa.
16. Ba kowace mace ke iya gaida mijinta da safe ba ganin sun kwana sun tashi tare, to kai koya ma taka saboda zuri'arka.
17. Yi murna da murna da murnarta, kar tana cikin murna kai kuma ka hade rai kamar tsohon kare.
18. Yi fira da ita, hakan zai sa ka gane matsalolinta.
19. Cika mata alkawuran da ka daukar mata zai kara kimarka a idanunta.
20. Yi mata binciken kwakwaf zai haddasa gaba da raini tsakaninku.
Allah ka bamu zuri'a ta gari...
PLS TYPE AMEEEN.
Ameeen Ya Allah.